Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 27:63 - Littafi Mai Tsarki

63 suka ce, “Ya mai girma, mun tuna yadda mayaudarin nan, tun yana da rai ya ce bayan kwana uku zai tashi daga matattu.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

63 Suka ce, “Ranka yă daɗe, mun tuna, mai ruɗin nan tun yana da rai ya ce, ‘Bayan kwana uku, zan tashi daga matattu.’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 27:63
18 Iomraidhean Croise  

Tun daga lokacin nan Yesu ya fara bayyana wa almajiransa, lalle ne ya tafi Urushalima, ya sha wuya iri iri a hannun shugabanni da manyan firistoci da malaman Attaura, har a kashe shi, a rana ta uku kuma a tashe shi.


za su kuwa kashe shi, a rana ta uku kuma za a tashe shi.” Sai duk tsananin baƙin ciki ya rufe su.


su bashe shi ga al'ummai, su yi masa ba'a, su yi masa bulala, su kuma gicciye shi. A rana ta uku kuma za a tashe shi.”


suka ce, “Wannan ya ce, wai zai iya rushe Haikalin nan na Allah, ya kuma gina shi a cikin kwana uku.”


Saboda haka sai ka yi umarni a tsare kabarin nan sosai har rana ta uku, kada almajiransa su sace shi, sa'an nan su ce wa mutane wai ya tashi daga matattu. Yaudarar ƙarshe za ta fi ta farkon muni ke nan.”


Ai, ba ya nan. Ya tashi, yadda ya faɗa. Ku zo ku ga wurin da aka sa shi.


Za su yi masa ba'a, su tofa masa yau, su yi masa bulala, su kashe shi, bayan kwana uku kuma ya tashi.”


Ya fara koya musu, cewa lalle ne Ɗan Mutum ya sha wuya iri iri, shugabanni, da manyan firistoci, da malaman Attaura su ƙi shi, har a kashe shi, bayan kwana uku kuma ya tashi da rai.


domin yana koya wa almajiransa ne, yana ce musu, “Za a ba da Ɗan Mutum ga mutane, za su kuwa kashe shi, sa'ad da aka kashe shi kuma, bayan kwana uku zai tashi.”


Sai ya keɓe sha biyun nan, ya ce musu, “Ga shi, za mu Urushalima, duk abin da yake rubuce kuma game da Ɗan Mutum, ta hannun annabawa zai tabbata.


Za su yi masa bulala, su kashe shi, a rana ta uku kuma ya tashi.”


Sai suka fara kai ƙararsa, suna cewa, “Mun sami mutumin nan yana ɓad da jama'armu, yana hana a biya Kaisar haraji, yana cewa, shi ne Almasihu, sarki kuma.”


Ya ce, “Lalle ne Ɗan mutum yă sha wuya iri iri, shugabanni da manyan firistoci da malaman Attaura su ƙi shi, har a kashe shi, a rana ta uku kuma a tashe shi.”


Yesu ya amsa musu ya ce, “Ku rushe Haikalin nan, ni kuwa in ta da shi a cikin kwana uku.”


Taro kuma suka riƙa maganarsa a raɗe, waɗansu na cewa, “Mutum ne nagari.” Waɗansu kuma na cewa, “A'a, ai, ɓad da jama'a yake.”


Sai Farisiyawa suka amsa musu suka ce, “Af! Har ku ma an ɓad da ku ne?


Ana ɗaukaka mu, ana kuma wulakanta mu, ana yabonmu, ana kuma kushenmu. An ɗauke mu kamar mayaudara, mu kuwa masu gaskiya ne.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan