Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 27:53 - Littafi Mai Tsarki

53 Suka firfito daga kaburburan, bayan ya tashi daga matattu, sai suka shiga tsattsarkan birnin, suka bayyana ga mutane da yawa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

53 Suka firfito daga kaburbura, sa’an nan bayan tashin Yesu daga matattu, suka shiga birni mai tsarki, suka bayyana ga mutane da yawa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 27:53
7 Iomraidhean Croise  

Shugabannin jama'a kuwa suka zauna a Urushalima. Sauran jama'a kuma suka jefa kuri'a don a sami mutum guda daga cikin goma wanda zai zauna a Urushalima, wato tsattsarkan birni, sauran tara kuwa su yi zamansu a sauran garuruwa.


Amma duk da haka kuna fāriya, da cewa Ku ne mazaunan birni mai tsarki, Kuna kuma dogara ga Allah na Isra'ila, Wanda sunansa Ubangiji, Mai Runduna.


“An ƙayyade wa jama'arka da tsattsarkan birninka shekara ɗari huɗu da tasa'in domin a kawo ƙarshen laifi da zunubi, domin a yi kafarar laifi, sa'an nan a shigo da adalci madawwami, a rufe wahayi da annabci, a tsarkake Haikali.


Sa'an nan Iblis ya kai shi tsattsarkan birni, ya ɗora shi can kan tsororuwar Haikali,


amma kada ka auna harabar Haikalin, ka ƙyale ta, domin an ba da ita ga al'ummai, za su tattake tsattsarkan birnin nan har wata arba'in da biyu.


Sai na ga tsattsarkan birni kuma, Sabuwar Urushalima, tana saukowa daga Sama daga wurin Allah, shiryayyiya kamar amaryar da ta yi ado saboda mijinta.


In kuma wani ya yi ragi a maganar littafin annabcin nan, Allah zai ɗauke rabonsa na itacen rai, da na tsattsarkan birnin, waɗanda aka rubuta a littafin nan.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan