49 Amma sauran suka ce, “Ku bari mu gani ko Iliya zai zo ya ceci shi.”
49 Sauran kuwa suka ce, “Ƙyale shi mu ga, ko Iliya zai zo yă cece shi.”
Wani annabi mai suna Iliya, mutumin Tishbi a Gileyad, ya ce wa sarki Ahab, “Na rantse da Ubangiji, Allah na Isra'ila, wanda nake bauta wa, ba za a yi raɓa ko ruwan sama cikin shekarun nan ba, sai da faɗata.”
Suna cewa, “Ai, Allah ya rabu da shi, Gama ba wanda zai cece shi!”
Sai nan da nan ɗaya daga cikinsu ya yiwo gudu, ya ɗauko soso ya jiƙa shi da ruwan tsami, ya soka a sanda, ya miƙa masa yă sha.
Sai Yesu ya sāke ɗaga murya da ƙarfi, sa'an nan ya săki ransa.