45 To, tun daga tsakar rana, duhu ya rufe ƙasa duka, har zuwa ƙarfe uku na yamma.
45 Daga sa’a ta shida, har zuwa sa’a ta tara, duhu ya rufe ƙasa duka.
Ina da iko in sa sararin sama ya yi duhu, In sa ya zama makoki domin matattu.”
A wannan lokaci rana za ta fāɗi da tsakar rana, Duniya ta duhunta da rana kata. Ni, Ubangiji ne na faɗa.
Da ƙarfe tara na safe suka gicciye shi.
Ran nan kuwa ranar shirin Idin Ƙetarewa ce, wajen tsakiyar rana. Sai ya ce wa Yahudawa, “Ga sarkinku!”
To, Bitrus da Yahaya suna tafiya Haikali a lokacin addu'a, da ƙarfe uku na yamma,
Mala'ika na huɗu ya busa ƙahonsa, sai aka bugi sulusin rana, da sulusin wata, da kuma sulusin taurari, har sulusin haskensu ya zama duhu, wato ba haske a sulusin yini, haka kuma a sulusin dare.
Ya kuwa buɗe ramin mahallakar, sai wani hayaƙi kamar na babbar matoya ya taso, har hayaƙin ramin nan ya duhunta rana da sararin sama.