Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 27:43 - Littafi Mai Tsarki

43 Yā dogara ga Allah, to, Allah ya cece shi mana yanzu, in dai yana sonsa, don ya ce wai shi Ɗan Allah ne.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

43 Ya dogara ga Allah. Bari Allah yă cece shi yanzu, in yana sonsa, domin ya ce, ‘Ni Ɗan Allah ne.’ ”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 27:43
17 Iomraidhean Croise  

Suna yi wa shirye-shiryen kāsasshe dariya, Saboda yana dogara ga Ubangiji.


Suka ce, “Ka dogara ga Ubangiji, Me ya sa bai cece ka ba? Idan Ubangiji na sonka, Don me bai taimake ka ba?”


Suna magana a kaina, suna cewa, “Allah ba zai taimake shi ba!”


An ragargaza ni da zargin maƙiyana Waɗanda suke tambayata kullum, “Ina Allahnka?”


Suna cewa, “Ai, Allah ya rabu da shi, Gama ba wanda zai cece shi!”


Kada kuma ku bari ya rinjaye ku ku dogara ga Ubangiji, har ku sa tsammani Ubangiji zai cece ku, ya hana sojojinmu na Assuriya su cinye birninku.


Kada ku bar Hezekiya ya ruɗe ku, da cewa Ubangiji zai kuɓutar da ku. Ko gumakan waɗansu al'ummai sun ceci ƙasashensu daga Sarkin Assuriya?


ya ce masa, “Allahn da kake dogara gare shi ya faɗa maka, ba za ka faɗa a hannuna ba, amma kada ka yarda wannan ya ruɗe ka.


suna cewa, “Kai da za ka rushe Haikalin, ka kuma gina shi a cikin kwana uku, ceci kanka mana! In kai Ɗan Allah ne, to sauko daga gicciyen mana!”


Sa'ad da jarumin da waɗanda suke tare da shi suna tsaron Yesu suka ga rawar ƙasa da kuma abin da ya auku, sai duk tsoro ya kama su, suka ce, “Hakika wannan Ɗan Allah ne!”


Mutane da suke tsaitsaye, suna kallo. Shugabanni kuma suka yi masa ba'a, suka ce, “Ya ceci waɗansu, to, ya ceci kansa mana, in shi ne Almasihu na Allah zaɓaɓɓensa!”


suna cewa, “In kai ne Sarkin Yahudawa, to, ka cece kanka mana!”


Ni da Uba ɗaya muke.”


kwa ce da wanda Uba ya keɓe, ya kuma aiko duniya, ‘Sāɓo kake,’ domin na ce, ‘Ni Ɗan Allah ne’?


Yahudawa suka amsa masa suka ce, “Ai, muna da Shari'a, bisa ga Sharian nan kuwa ya wajaba a kashe shi, saboda ya mai da kansa Ɗan Allah.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan