Mattiyu 27:41 - Littafi Mai Tsarki41 Haka kuma manyan firistoci da malaman Attaura da shugabanni suka riƙa yi masa ba'a, suna cewa, Faic an caibideilSabon Rai Don Kowa 202041 Haka ma, manyan firistoci da malaman dokoki da kuma dattawa, suka yi ta yin masa ba’a, suna cewa, Faic an caibideil |
Allah Mai Tsarki na Isra'ila, Mai Fansa, Ya ce wa wanda aka raina ƙwarai, Al'ummai suka ƙi shi, Bawa na masu mulki kuma, “Sarakuna za su gan ka a sake, Su kuma miƙe tsaye su ba ka girma, Shugabanni su kuma za su gani, Su rusuna har ƙasa su ba ka girma.” Wannan kuwa zai faru saboda Ubangiji, Allah Mai Tsarki na Isra'ila, ya zaɓi bawansa, Ya kuwa cika alkawaransa.