In da a ce a matsayina kake, ni kuma ina a naka, Ina iya faɗar duk abin da kake faɗa yanzu. Da sai in kaɗa kaina da hikima, In dulmuyar da kai a cikin rigyawar maganganu.
Zuciyata ta karai saboda cin mutuncin da ake ci mini, Ni kuwa ba ni da mataimaki, Na sa zuciya za a kula da ni, Amma babu. Na sa zuciya zan sami ta'aziyya, Amma ban samu ba.
“Dukanku masu wucewa, ba wani abu ba ne a gare ku? Ku duba, ku gani, ko akwai baƙin ciki irin nawa, Wanda Ubangiji ya ɗora mini, A ranar fushinsa mai zafi.