Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 27:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Sa'ad da Yahuza mai bashe shi ya ga an yanke masa hukuncin kisa, sai ya yi nadama, ya mayar wa manyan firistoci da shugabanni da kuɗi azurfa talatin ɗin nan,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Sa’ad da Yahuda, wanda ya bashe Yesu, ya ga an yanke wa Yesu hukuncin kisa, sai ya yi “da na sani.” Ya je mayar wa manyan firistoci da dattawan kuɗin azurfa talatin ɗin.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 27:3
15 Iomraidhean Croise  

Ba wani mugun mutum wanda ya taɓa daɗewa da farin ciki.


Idan san ya kashe bawa ko baiwa, sai mai san ya biya wa ubangijin bawan, ko baiwar, shekel talatin a kuma jajjefi san.


Ubangiji kuma ya ce mini, “Ka zuba kuɗin a baitulmalin Haikali.” Sai na ɗauki kuɗin da suka kimanta shi ne tamanina, na zuba su a baitulmalin Haikalin Ubangiji.


Ana cikin cin abincin dare, Iblis kuwa ya riga ya sa a zuciyar Yahuza Iskariyoti ɗan Saminu yă bāshe shi.


Da karɓar 'yar loman nan Shaiɗan ya shige shi. Yesu ya ce masa, “Yi abin da za ka yi, maza.”


Yahuza kuwa bayan ya ɗauko ƙungiyar soja, da waɗansu dogaran Haikali daga manyan firistoci da Farisiyawa, suka zo wurin, riƙe da fitilu, da jiniyoyi, da makamai,


(To, shi mutumin nan, da ladan mugun aikinsa ya sayi wani fili, sai ya fāɗi da kā, cikinsa ya fashe, kayan cikinsa duk suka zubo.


Don baƙin ciki irin wanda Allah yake sawa, shi ne yake biyarwa zuwa ga tuba, da kuma samun ceto, ba ya kuma sa “da na sani”. Amma baƙin ciki a kan al'amarin duniya, yakan jawo mutuwa.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan