Mattiyu 27:29 - Littafi Mai Tsarki29 Suka yi wani rawani na ƙaya, suka sa masa a kā, suka danƙa masa sanda a hannunsa na dama, suka kuma durƙusa a gabansa, suna yi masa ba'a suna cewa, “Ranka ya daɗe, Sarkin Yahudawa!” Faic an caibideilSabon Rai Don Kowa 202029 Suka kuma tuƙa wani rawanin ƙaya, suka sa masa a kā. Suka sa sanda a hannun damansa. Suka durƙusa a gabansa, suka yi masa ba’a, suna cewa, “Ranka yă daɗe sarkin Yahudawa!” Faic an caibideil |
Allah Mai Tsarki na Isra'ila, Mai Fansa, Ya ce wa wanda aka raina ƙwarai, Al'ummai suka ƙi shi, Bawa na masu mulki kuma, “Sarakuna za su gan ka a sake, Su kuma miƙe tsaye su ba ka girma, Shugabanni su kuma za su gani, Su rusuna har ƙasa su ba ka girma.” Wannan kuwa zai faru saboda Ubangiji, Allah Mai Tsarki na Isra'ila, ya zaɓi bawansa, Ya kuwa cika alkawaransa.