Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 27:22 - Littafi Mai Tsarki

22 Bilatus ya ce musu, “To, ƙaƙa zan yi da Yesu da ake kira Almasihu?” Duk sai suka ce, “A gicciye shi!”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

22 Bilatus ya yi tambaya, “To, me zan yi da Yesu wanda ake kira Kiristi?” Duka suka ce, “A gicciye shi!”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 27:22
16 Iomraidhean Croise  

Ko mutanen da suke cikin alfarwata ba wanda zai ce, Ga wani can da bai ƙoshi da nama ba.


Allah Mai Tsarki na Isra'ila, Mai Fansa, Ya ce wa wanda aka raina ƙwarai, Al'ummai suka ƙi shi, Bawa na masu mulki kuma, “Sarakuna za su gan ka a sake, Su kuma miƙe tsaye su ba ka girma, Shugabanni su kuma za su gani, Su rusuna har ƙasa su ba ka girma.” Wannan kuwa zai faru saboda Ubangiji, Allah Mai Tsarki na Isra'ila, ya zaɓi bawansa, Ya kuwa cika alkawaransa.


A wata guda na hallaka makiyayan nan uku, gama ban jure da su ba, su ma sun gaji da ni.


Yakubu ya haifi Yusufu mijin Maryamu wadda ta haifi Yesu, wanda ake kira Almasihu.


Da suka taru sai Bilatus ya ce musu, “Wa kuke so in sakar muku? Barabbas ko kuwa Yesu da ake kira Almasihu?”


Sai mai mulki ya sāke ce musu, “Wane ne a cikin biyun nan kuke so in sakar muku?” Sai suka ce, “Barabbas.”


Ya ce, “Ta wane halin? Wane mugun abu ya yi?” Amma su sai ƙara ɗaga murya suke ta yi, suna cewa, “A gicciye shi!”


To, manyan firistoci da 'yan majalisa duka suka nemi shaidar da za a tabbatar a kan Yesu, don su samu su kashe shi, amma ba su samu ba.


Sai matar ta ce masa, “Na san Masihi yana zuwa, wanda ake kira Almasihu. Sa'ad da ya zo kuwa, zai sanar da mu kome.”


Ko da yake ba su same shi da wani laifin kisa ba, duk da haka suka roƙi Bilatus a kashe shi.


Saboda haka, 'yan'uwa, sai ku sani albarkacin mutumin nan ne ake sanar da ku gafarar zunubanku.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan