Sa'ad da suka zo wurin da Allah ya faɗa masa, sai Ibrahim ya gina bagade a can, ya jera itace a kai. Ya ɗaure Ishaku ɗansa, ya sa shi a bisa itacen bagaden.
Sai suka yi ta haƙwansa, suka aiki 'yan rahoto, su kuwa suka nuna kamar su masu adalci ne, da nufin su kama shi a maganarsa, su kuma ba da shi ga mai mulki ya hukunta shi.
A shekara ta goma sha biyar ta mulkin Kaisar Tibariyas, Buntus Bilatus yana mulkin Yahudiya, Hirudus yana sarautar Galili, ɗan'uwansa Filibus yana sarauta Ituriya da Tarakunitas, Lisaniyas kuma yana sarautar Abiliya,
Daga wurin Kayafa kuma suka kai Yesu fādar mai mulki. Da asuba ne kuwa. Su kansu ba su shiga fādar ba, wai don kada su ƙazantu su kāsa cin jibin Ƙetarewa.
A daren da in gari ya waye Hirudus yake da niyyar fito da shi a yi masa hukunci, Bitrus kuwa na barci a tsakanin soja biyu, ɗaure da sarƙa biyu, masu tsaro kuma suna bakin ƙofa suna tsaron kurkukun,
Bayan sun ɗaɗɗaure shi da tsirkiya, Bulus ya ce wa jarumin ɗin da yake tsaye kusa, “Ashe, ya halatta a gare ka ka yi wa mutumin da yake da 'yancin Roma bulala, ba ko bin ba'asi?”
Saboda haka, waɗanda suke shirin tuhumarsa, suka rabu da shi nan da nan. Shi ma shugaban da ya fahimci Bulus Barome ne, sai ya tsorata, ga shi kuwa, ya ɗaure shi.
Allahn Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, Allahn kakanninmu, shi ya ɗaukaka Baransa Yesu, wanda kuka bashe shi, kuka kuma ƙi shi, a gaban Bilatus, sa'ad da ya ƙudura zai sake shi.
Gama hakika Hirudus da Buntus Bilatus sun haɗa kai a birnin nan tare da al'ummai da jama'ar Isra'ila gāba da Yesu Baranka mai tsarki, wanda ka maishe shi Almasihu.
Suka ce masa, “Mun gangara zuwa wurinka don mu ɗaure ka, mu miƙa ka gare su.” Samson ya ce musu, “Ku rantse mini idan ba ku ne da kanku kuke so ku kashe ni ba.”