Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 26:75 - Littafi Mai Tsarki

75 Sai Bitrus ya tuna da maganar Yesu cewa, “Kafin carar zakara za ka yi musun sanina sau uku.” Sai ya fita waje, ya yi ta rusa kuka.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

75 Sai Bitrus ya tuna da maganar da Yesu ya yi cewa, “Kafin zakara yă yi cara, za ka yi mūsun sani na sau uku.” Sai ya fita waje, ya yi ta kuka.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 26:75
11 Iomraidhean Croise  

Duk wanda kuwa ya yi musun sanina a gaban mutane, ni ma zan yi musun saninsa a gaban Ubanmu da yake cikin Sama.”


Yesu ya ce masa, “Hakika, ina gaya maka, ko a wannan dare, kafin carar zakara, za ka yi musun sanina sau uku.”


Sai ya fara la'anar kansa, yana ta rantse-rantse, yana cewa, “Ban ma san mutumin nan ba.” Nan da nan sai zakara ya yi cara.


Yesu ya amsa ya ce, “Ashe, za ka ba da ranka saboda ni? Lalle hakika, ina gaya maka, kafin zakara ya yi cara, za ka yi musun sanina sau uku.”


Wa ya fifita ka da sauran? Me kuma kake da shi, wanda ba karɓa ka yi ba? Da yake karɓa ka yi, don me kake fahariya, kamar ba karɓa ka yi ba?


Ya ku 'yan'uwa, in an kama mutum yana a cikin yin laifi, ku da kuke na ruhu, sai ku komo da shi a kan hanya da tawali'u, kowa yana kula da kansa kada shi ma ya burmu.


wato, ku da ikon Allah yake kiyayewa ta wurin bangaskiyarku, domin samun ceton nan da aka shirya a bayyana a ƙarshen zamani.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan