Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 26:72 - Littafi Mai Tsarki

72 Sai ya sāke musawa har da rantsuwa ya ce, “Ban ma san mutumin nan ba.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

72 Ya sāke mūsu har da rantsuwa, yana cewa, “Ban ma san mutumin nan ba!”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 26:72
11 Iomraidhean Croise  

“Kada ka kama sunan Ubangiji Allahnka a banza, gama zan hukunta duk wanda ya kama sunana a banza.


Ku kasa kunne, ya jama'ar Isra'ila, Ku da kuke zuriyar Yahuza. Kuna rantsuwa da sunan Ubangiji, Kuna nuna kamar kuna sujada ga Allah na Isra'ila, Amma abin da kuke faɗa ba haka kuke nufi ba.


Kada ku ƙulla wa junanku sharri, kada kuma ku so yin rantsuwa ta ƙarya, gama ina ƙin waɗannan abubuwa duka, ni Ubangiji na faɗa.”


Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Zan zo wurinku domin in yi shari'a. Nan da nan zan tabbatar da laifin masu yin sihiri, da na mazinata, da na masu shaidar zur, da na masu zaluntar ma'aikata a kan albashinsu, da waɗanda suke ƙwarar gwauraye, wato matan da mazansu suka mutu, da marayu, da baƙi, da waɗanda ba su ganin girmana.”


Da ya fito zaure, sai wata baranya kuma ta gan shi, ta ce wa waɗanda suke tsaitsaye a wurin, “Ai, mutumin nan tare yake da Yesu Banazare!”


Jim kaɗan sai na tsaitsayen suka matso, suka ce wa Bitrus, “Lalle kai ma ɗayansu ne, don irin maganarka ta tona ka.”


Sai ya fara la'anar kansa, yana ta rantse-rantse, yana cewa, “Ban ma san mutumin nan ba.” Nan da nan sai zakara ya yi cara.


Yesu ya ce, “Ina dai gaya maka Bitrus, a yau ma, kafin carar zakara, za ka yi musun sanina sau uku.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan