68 suna cewa, “Yi mana annabci, kai Almasihu! Faɗi wanda ya buge ka!”
68 suka ce, “Yi mana annabci, Kiristi. Wa ya buge ka?”
Sai suka tattofa masa yau a fuska, suka bubbuge shi, waɗansu kuma suka mammare shi,
Waɗansu ma suka fara tattofa masa yau, suka ɗaure masa idanu, suka bubbuge shi, suna ce masa, “Yi annabci!” Dogaran Haikali kuma suka yi ta marinsa.
Sa'ad da suke ta farin ciki, sai suka ce, “A kawo Samson ya yi mana wasa.” Sai suka kawo Samson daga kurkuku, ya kuwa yi wasa a gabansu. Suka sa ya tsaya a tsakanin ginshiƙai.