Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 26:65 - Littafi Mai Tsarki

65 Sai babban firist ya kyakketa tufafinsa, ya ce, “Ya yi saɓo! Wace shaida kuma za mu nema? Yanzu kun ji saɓon da ya yi!

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

65 Sa’an nan babban firist ya yage tufafinsa ya ce, “Ya yi saɓo! Don me muke bukatar ƙarin shaidu? Ga shi, yanzu kun dai ji saɓon.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 26:65
12 Iomraidhean Croise  

Sa'an nan Eliyakim ɗan Hilkiya, wanda yake wakilin gidan sarki, da Shebna magatakarda, da Yowa ɗan Asaf marubuci, suka zo wurin Hezekiya da tufafinsu ketattu, suka faɗa masa irin maganar da Rabshake ya yi.


Duk da haka da sarkin da barorinsa suka ji maganar, ba wanda ya ji tsoro, balle su keta rigunansu don baƙin ciki.


ko mai ƙusumbi, ko wada, ko mai lahani a ido, ko cuta mai sa ƙaiƙayi, ko kirci, ko dandaƙaƙƙe, ba zai kusato garin ya miƙa hadaya ba.


Sai Joshuwa, ɗan Nun, da Kalibu, ɗan Yefunne waɗanda suke tare da masu leƙo asirin ƙasar, suka yayyage tufafinsu.


Sai waɗansu malaman Attaura suka ce a ransu, “Wannan mutum, ai, saɓo yake!”


Sai malaman Attaura da Farisiyawa suka fara wuswasi cewa, “Wane ne wannan da yake maganar saɓo? Wa yake iya gafarta zunubi banda Allah shi kaɗai?”


Yahudawa suka amsa suka ce, “Ba don wani aiki nagari za mu jajjefe ka ba, sai don sāɓo, don kai, ga ka mutum, amma kana mai da kanka Allah.”


kwa ce da wanda Uba ya keɓe, ya kuma aiko duniya, ‘Sāɓo kake,’ domin na ce, ‘Ni Ɗan Allah ne’?


Amma da manzannin nan, Barnaba da Bulus, suka ji haka, suka kyakketa tufafinsu, suka ruga cikin taron, suna ɗaga murya suna cewa,


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan