Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 26:58 - Littafi Mai Tsarki

58 Amma Bitrus ya bi shi daga nesa, har cikin gidan babban firist. Da ya shiga, sai ya zauna tare da dogaran Haikali, don ya ga ƙarshen abin.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

58 Amma Bitrus ya bi daga nesa, har zuwa cikin filin gidan babban firist. Ya shiga, ya zauna tare da masu gadi, don yă ga ƙarshen abin.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 26:58
10 Iomraidhean Croise  

Sai manyan firistoci da shugabannin jama'a suka taru a gidan babban firist, mai suna Kayafa.


Ka hanzarta shiryawa da mai ƙararka tun kuna tafiya gaban shari'a, don kada mai kararka ya bashe ka ga alƙali, alƙali kuma ya miƙa ka ga dogari, a kuma jefa ka a kurkuku.


Sai suka kama shi, suka tafi da shi, suka kai shi cikin gidan babban firist. Bitrus kuwa yana biye daga nesa nesa.


To, Bitrus kuwa yana tsaye yana jin wuta. Sai suka ce masa, “Anya! Kai ma ba cikin almajiransa kake ba?” Sai ya mūsu ya ce, “A'a, ba na ciki.”


Da manyan firistoci da dogaran Haikali suka gan shi, suka ɗau kururuwa suna cewa, “A gicciye shi! A gicciye shi!” Bilatus ya ce musu, “Ku tafi da shi ku da kanku, ku gicciye shi, ni kam, ban same shi da wani laifi ba.”


Farisiyawa suka ji taro suna raɗeraɗinsa haka, sai manyan firistoci da Farisiyawa suka aiki dogaran Haikali su kamo shi.


Daga nan dogaran Haikali suka koma wurin manyan firistoci da Farisiyawa, su kuwa suka ce musu, “Don me ba ku kawo shi ba?”


Amma da dogaran Haikali suka je, ba su same su a kurkukun ba, suka dawo suka ba da labari, suka ce,


Sai shugaban dogaran Haikali da dogaran suka je suka kawo manzannin, amma fa ba ƙarfi da yaji ba, don suna tsoro kada jama'a su jejjefe su da duwatsu.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan