Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 26:55 - Littafi Mai Tsarki

55 Nan take Yesu ya ce wa taron jama'a, “Kun fito ne da takuba da kulake ku kama ni kamar ɗan fashi? Kowace rana nakan zauna a Haikali ina koyarwa, amma ba ku kama ni ba.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

55 A wannan lokaci sai Yesu ya ce wa taron, “Ina jagoran wani tawaye ne, da kuka fito da takuba da kuma sanduna domin ku kama ni? Kowace rana ina zama a filin haikali ina koyarwa, ba ku kuwa kama ni ba.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 26:55
15 Iomraidhean Croise  

Ya shiga Haikali yana cikin koyarwa, sai manyan firistoci da shugabannin jama'a suka zo wurinsa, suka ce, “Da wane izini kake yin abubuwan nan, wa ya ba ka izinin?”


Kafin ya rufe baki ga Yahuza, ɗaya daga cikin sha biyun nan, da babban taron mutane riƙe da takuba da kulake, manyan firistoci da shugabanni ne suka turo su.


Sai Yesu ya tashi daga nan, ya tafi ƙasar Yahudiya, da kuma hayin Kogin Urdun. Taro kuma ya sāke haɗuwa wurinsa, ya kuma sāke koya musu kamar yadda ya saba.


Sa'ad da Yesu yake koyarwa a Haikalin sai ya ce, “Ƙaƙa malaman Attaura za su ce Almasihu ɗan Dawuda ne?


Kowace rana ya yi ta koyarwa a Haikali. Amma manyan firistoci, da malaman Attaura, da shugabannin jama'a suka nema su hallaka shi.


Wata rana yana koyar da mutane a Haikali, yana yi musu bishara, sai ga manyan firistoci da malaman Attaura, da shugabanni suka matso,


Ya rufe littafin ya mayar wa mai hidima, ya zauna. Duk waɗanda suke cikin majami'a suka zuba masa ido.


Wajen tsakiyar idin sai Yesu ya shiga Haikali ya koyar.


Yesu yana koyarwa a Haikalin ke nan, sai ya ɗaga murya ya ce, “Kun dai san ni, kun kuma san daga inda nake. Ban fa zo domin kaina ba. Wanda ya aiko ni mai gaskiya ne, shi kuwa ba ku san shi ba.


Da sassafe kuma ya sāke shiga Haikali. Duk mutane suka zo wurinsa, ya kuwa zauna yana koya musu.


Ya faɗi wannan magana ne a baitulmalin Haikali, lokacin da yake koyarwa a wurin. Duk da haka ba wanda ya kama shi, don lokacinsa bai yi ba tukuna.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan