“Ka farka, ya kai takobi, ka fāɗa wa makiyayina, Ka fāɗa wa mutumin da yake kusa da ni, Ka sari makiyayin domin tumakin su watse. Zan bugi ƙanana da hannuna, Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.
Yesu ya ce musu, “Ashe, ba ku taɓa karantawa a Littattafai ba? cewa, “ ‘Dutsen da magina suka ƙi, Shi ne ya zama mafificin dutsen gini. Wannan aikin Ubangiji ne, A gare mu kuwa abin al'ajabi ne.’
Ɗan Mutum zai tafi ne, yadda labarinsa yake a rubuce, duk da haka kaiton mutumin nan da yake ba da Ɗan Mutum! Da ma ba a haifi mutumin nan ba, da zai fiye masa.”