Kafin ya rufe baki ga Yahuza, ɗaya daga cikin sha biyun nan, da babban taron mutane riƙe da takuba da kulake, manyan firistoci da shugabanni ne suka turo su.
Sai Bitrus ya waiwaya ya ga almajirin nan da Yesu yake ƙauna yana biye da su, wato wanda ya jingina gab da Yesu lokacin cin jibin nan da ya ce, “Ya Ubangiji, wane ne zai bāshe ka?”
Sai Bulus ya amsa ya ce, “Me ke nan kuke yi, kuna kuka kuna baƙanta mini rai? Ai, ni a shirye nake, ba wai a ɗaure ni kawai ba, har ma a kashe ni a Urushalima saboda sunan Ubangiji Yesu.”