Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 26:41 - Littafi Mai Tsarki

41 Ku zauna a faɗake, ku yi addu'a, kada ku faɗa ga gwaji. Lalle ruhu ya ɗauka, amma jiki rarrauna ne.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

41 Ku yi tsaro, ku kuma yi addu’a, don kada ku fāɗi cikin jarraba. Ruhu yana so, sai dai jiki raunana ne.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 26:41
34 Iomraidhean Croise  

Masu farin ciki ne, marasa laifi cikin zamansu, Waɗanda suke zamansu bisa ga dokar Ubangiji.


Ku rabu da ni, ku masu zunubi! Zan yi biyayya da umarnan Allahna.


Ka riƙe ni, sai in zauna lafiya, Koyaushe zan mai da hankali ga umarnanka.


Ina ɗokin yin biyayya da umarnanka, Gama za ka ƙara mini fahimi.


To, ku zauna a faɗake fa, don ba ku san ranar da Ubangijinku zai dawo ba.


Don haka, sai ku zauna a faɗake, don ba ku san ranar ba, ko kuwa sa'ar.”


Sai ya ce musu, “Raina yana shan wahala matuƙa, har ma kamar in mutu. Ku dakata a nan, ku zauna a faɗake tare da ni.”


Kada ka kai mu wurin jaraba, Amma ka cece mu daga Mugun.’


Ku zauna a faɗake, ku yi addu'a kada ku faɗa ga gwaji. Lalle ruhu ya ɗauka, amma jiki rarrauna ne.”


Ka gafarta mana zunubanmu, gama mu ma muna gafarta wa duk wanda yake yi mana laifi. Kada ka kai mu wurin jaraba.’ ”


Koyaushe ku zauna a faɗake, kuna addu'a ku sami ikon tsere wa dukan waɗannan al'amura da za su auku, ku kuma tsaya a gaban Ɗan Mutum.”


Da ya iso wurin, ya ce musu, “Ku yi addu'a, kada ku faɗa ga gwaji.”


Sai ya ce musu, “Don me kuke barci? Ku tashi, ku yi addu'a, kada ku faɗa ga gwaji.”


Na kan dutsen kuwa su ne waɗanda da zarar sun ji Maganar, sai su karɓa da farin ciki. Su kam, ba su da tushe. Sukan ba da gaskiya 'yan kwanaki kaɗan, amma a lokacin gwaji, sai su bauɗe.


Abin da ba shi yiwuwa Shari'a ta yi domin ta kasa saboda halin ɗan adam, Allah ya yi shi, wato ya ka da zunubi a cikin jiki, da ya aiko da Ɗansa da kamannin jikin nan namu mai zunubi, domin kawar da zunubi.


Ba wani gwajin da ya taɓa samunku, wanda ba a saba yi wa ɗan adam ba. Allah mai alkawari ne, ba zai kuwa yarda a gwada ku fin ƙarfinku ba, amma a game da gwajin sai ya ba da mafita, yadda za ku iya jure shi.


Ku zauna a faɗake, ku dāge ga bangaskiyarku, ku yi ƙwazo, ku yi ƙarfi.


Amma ina azabta jikina ne, don in bautar da shi, kada bayan da na yi wa waɗansu wa'azi, ni da kaina a yar da ni.


Waɗanda kuwa suke su na Almasihu Yesu ne, sun gicciye halin mutuntaka da mugayen sha'awace-sha'awace iri iri.


a koyaushe kuna addu'a da roƙo ta wurin ikon Ruhu ba fāsawa. A kan wannan manufa ku tsaya da kaifinku da matuƙar naci, kuna yi wa dukan tsarkaka addu'a.


Ƙarshen dukan abubuwa ya gabato. Saboda haka, sai ku kanku, ku natsu, domin ku yi addu'a.


Ku natsu, ku kuma zauna a faɗake. Magabcinku Iblis yana zazzāgawa kamar zaki mai ruri, yana neman wanda zai lanƙwame.


ashe kuwa, Ubangiji ya san yadda zai kuɓutar da masu tsoronsa daga gwaje-gwaje, ya kuma tsare marasa adalci a kan jiran hukunci, har ya zuwa ranar shari'a,


(“Ga ni nan a tafe kamar ɓarawo! Albarka tā tabbata ga wanda yake a zaune a faɗake, yana saye da tufafinsa, don kada ya tafi tsirara, a ga tsiraicinsa.”)


Tun da yake ka kiyaye maganar da na yi maka ta yin jimiri, Ni ma zan kiyaye ka daga sharrin lokacin nan na gwaji, wanda zai auko wa dukan duniya, don a gwada mazaunan duniya.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan