Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 26:40 - Littafi Mai Tsarki

40 Ya komo wurin almajiran, ya ga suna barci, sai ya ce wa Bitrus, “Ashe, ba za ku iya zama a faɗake tare da ni ko da na sa'a ɗaya ba?

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

40 Sa’an nan ya komo wurin almajiransa, ya tarar suna barci. Ya tambayi Bitrus ya ce, “Ashe, ba za ku iya yin tsaro tare da ni ko na sa’a guda ba?

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 26:40
12 Iomraidhean Croise  

Sarki Ahab ya amsa, ya ce, “Ku faɗa masa, sojan ainihi, sai ya gama yaƙi sa'an nan ya yi fāriya, amma ba tun kafin a fara ba.”


Ina barci, amma zuciyata na a farke, Sai na ji ƙaunataccena yana ƙwanƙwasa ƙofa. Buɗe mini in shigo, ƙaunatacciyata, budurwata, kurciyata, Wadda ba wanda zai kushe ki. Kaina ya jiƙe da raɓa, Gashina ya yi danshi da laimar ƙāsashi.


Da yake angon ya yi jinkiri, duk sai suka yi gyangyaɗi, har barci ya share su.


Bitrus ya ce masa, “Ko za a kashe ni tare da kai, ba zan yi musun saninka ba.” Haka ma duk almajiran suka ce.


Sai ya ce musu, “Raina yana shan wahala matuƙa, har ma kamar in mutu. Ku dakata a nan, ku zauna a faɗake tare da ni.”


Ku zauna a faɗake, ku yi addu'a, kada ku faɗa ga gwaji. Lalle ruhu ya ɗauka, amma jiki rarrauna ne.”


Har yanzu dai ya dawo ya ga suna barci, don duk barci ya cika musu ido.


Ya komo ya samu suna barci, sai ya ce wa Bitrus, “Bitrus, barci kake? Ashe, ba za ka iya zama a faɗake ko da sa'a ɗaya ba?


Da ya tashi daga addu'a, ya koma wurin almajiran, ya tarar suna barci saboda baƙin ciki.


Sai kuma Bitrus da waɗanda suke tare da shi, barci ya cika musu ido, amma da suka farka suka ga ɗaukakarsa, da kuma mutum biyun nan tsaye tare da shi.


Sa'an nan gobe da safe, da fitowar rana, ku tashi ku fāɗa wa birnin. Idan Ga'al da mutanen da suke tare da shi, suka fito, su kara da kai, ka fatattake su yadda ka iya!”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan