Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 26:35 - Littafi Mai Tsarki

35 Bitrus ya ce masa, “Ko za a kashe ni tare da kai, ba zan yi musun saninka ba.” Haka ma duk almajiran suka ce.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

35 Bitrus ya furta, “Ko da ma zan mutu ne tare da kai, ba zan taɓa yin mūsun saninka ba.” Dukan sauran almajiran ma suka faɗa haka.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 26:35
10 Iomraidhean Croise  

Dukan jama'a kuwa suka amsa masa baki ɗaya, suka ce, “Dukan abin da Ubangiji ya faɗa za mu aikata.” Musa kuwa ya mayar wa Ubangiji da amsar da jama'ar suka bayar.


Mutumin da yake tsoron Ubangiji ko yaushe, zai yi farin ciki, amma idan ya taurare zai lalace.


Girmankan mutum zai jawo masa ƙasƙanci, amma za a girmama mai tawali'u.


Duk wanda kuwa ya yi musun sanina a gaban mutane, ni ma zan yi musun saninsa a gaban Ubanmu da yake cikin Sama.”


Bitrus ya ce masa, “Ya Ubangiji, don me, ba zan iya binka a yanzu ba? Ai, zan ba da raina saboda kai.”


Hakika haka ne, amma saboda rashin bangaskiyarsu ne aka sare su, kai kuwa saboda bangaskiyarka ne kake kafe. Kada fa ka nuna alfarma, sai dai ka ji tsoron Allah.


Don haka duk wanda yake tsammani ya kahu, ya mai da hankali kada ya fāɗi.


Saboda haka, ya ƙaunatattuna, kamar yadda a kullum kuke biyayya, haka kuma yanzu, ku yi ta yin aikin ceton nan naku da halin bangirma tare da matsananciyar kula, ba ma sai ina nan kawai ba, har ma fiye da haka in ba na nan.


Da yake kuna kiransa Uba a wajen addu'a, shi da yake yi wa kowa shari'a gwargwadon aikinsa, ba zaɓe, sai ku ƙarasa lokacin baƙuncinku, kuna tsoronsa.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan