Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 26:34 - Littafi Mai Tsarki

34 Yesu ya ce masa, “Hakika, ina gaya maka, ko a wannan dare, kafin carar zakara, za ka yi musun sanina sau uku.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

34 Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake gaya maka, a daren nan, kafin zakara yă yi cara, za ka yi mūsun sanina sau uku.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 26:34
7 Iomraidhean Croise  

Bitrus ya ce masa, “Ko duk sun yi tuntuɓe sabili da kai, ni kam ba zan yi tuntuɓe ba faufau.”


Sai Bitrus ya tuna da maganar Yesu cewa, “Kafin carar zakara za ka yi musun sanina sau uku.” Sai ya fita waje, ya yi ta rusa kuka.


Nan da nan sai zakara ya yi cara ta biyu. Bitrus kuwa ya tuna da maganar da Yesu ya faɗa masa cewa, “Kafin zakara ya yi cara ta biyu, za ka yi musun sanina sau uku.” Ko da ya tuno haka, sai ya fashe da kuka.


Yesu ya ce, “Ina dai gaya maka Bitrus, a yau ma, kafin carar zakara, za ka yi musun sanina sau uku.”


Sai Ubangiji ya juya ya dubi Bitrus. Bitrus kuwa ya tuna da maganar da Ubangiji ya faɗa masa cewa, “A yau ma kafin carar zakara, za ka yi musun sanina sau uku.”


Yesu ya amsa ya ce, “Ashe, za ka ba da ranka saboda ni? Lalle hakika, ina gaya maka, kafin zakara ya yi cara, za ka yi musun sanina sau uku.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan