Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 26:33 - Littafi Mai Tsarki

33 Bitrus ya ce masa, “Ko duk sun yi tuntuɓe sabili da kai, ni kam ba zan yi tuntuɓe ba faufau.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

33 Bitrus ya amsa ya ce, “Ko da duka sun ja da baya saboda kai, ba zan taɓa ja da baya ba.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 26:33
15 Iomraidhean Croise  

Ina tafiya a kan tafarkinka kullum, Ban kuwa kauce ba.


Kowa gani yake shi mai biyayya ne, mai aminci. Amma ina? Ko ka yi ƙoƙari ka sami amintacce ɗaya daga cikinsu, ba za ka samu ba.


“Zuciya ta fi kome rikici, Cuta gare ta matuƙa, Wa zai san kanta?


Amma fa bayan an tashe ni, zan riga ku zuwa ƙasar Galili.”


Yesu ya ce masa, “Hakika, ina gaya maka, ko a wannan dare, kafin carar zakara, za ka yi musun sanina sau uku.”


Bitrus ya ce masa, “Ko duk sun yi tuntuɓe, ni kam, ba zan yi ba.”


Bitrus ya ce masa, “Ya Ubangiji, a shirye nake in bi ka har cikin kurkuku, ko kuma Lahira.”


Da suka karya kumallo Yesu ya ce wa Bitrus, “Bitrus ɗan Yahaya, ka fi waɗannan ƙaunata?” Ya ce masa, “I, ya Ubangiji, ka dai sani ina sonka.” Yesu ya ce masa, “Ka yi kiwon 'ya'yan tumakina.”


A game da ƙaunar 'yan'uwa kuwa, ku ƙaunaci juna gaya. A wajen ba da girma, kowa yă riga ba ɗan'uwansa.


Kada ku yi kome da sonkai ko girmankai, sai dai da tawali'u, kowa yana mai da ɗan'uwansa ya fi shi.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan