Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 26:31 - Littafi Mai Tsarki

31 Sai Yesu ya ce musu, “Duk za ku yi tuntuɓe sabili da ni a wannan dare domin a rubuce yake cewa, ‘Zan bugi makiyayi, tumakin garken kuwa za su fasu.’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

31 Sai Yesu ya ce musu, “A wannan dare, dukanku za ku ja da baya saboda ni, gama a rubuce yake cewa, “ ‘Zan bugi makiyayin, tumakin garken kuwa za su fasu.’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 26:31
16 Iomraidhean Croise  

Abokaina da maƙwabtana ba su ko zuwa kusa da ni, saboda miyakuna, Har iyalina ma sun guje mini.


Zuciyata ta karai saboda cin mutuncin da ake ci mini, Ni kuwa ba ni da mataimaki, Na sa zuciya za a kula da ni, Amma babu. Na sa zuciya zan sami ta'aziyya, Amma ban samu ba.


Ka sa har abokaina na kusa sun yashe ni, Duhu ne kaɗai abokin zamana.


Ubangiji ya ce, “Nufina ne ya sha wahala, Mutuwar kuwa hadaya ce domin ta kawo gafara, Saboda haka zai ga zuriyarsa, Zai yi tsawon rai, Ta wurinsa nufina zai cika.


“Na kira masoyana, amma suka yaudare ni, Firistocina da dattawana a cikin birni sun hallaka Saboda neman abincin da za su ci su rayu.


“Ka farka, ya kai takobi, ka fāɗa wa makiyayina, Ka fāɗa wa mutumin da yake kusa da ni, Ka sari makiyayin domin tumakin su watse. Zan bugi ƙanana da hannuna, Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.


Albarka tā tabbata ga wanda ba ya tuntuɓe sabili da ni.”


Ɗan Mutum zai tafi ne, yadda labarinsa yake a rubuce, duk da haka kaiton mutumin nan da yake ba da Ɗan Mutum! Da ma ba a haifi mutumin nan ba, da zai fiye masa.”


Amma duk wannan ya auku ne domin a cika littattafan annabawa.” Daga nan duk almajiran suka yashe shi, suka yi ta kansu.


To, lokaci na zuwa, har ma ya yi, da za a warwatsa ku, kowa yă koma gidansu, ku bar ni ni kaɗai. Duk da haka kuwa ba ni kaɗai nake ba, domin Uba na tare da ni.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan