30 Da suka yi waƙar yabon Allah, sai suka fita suka tafi Dutsen Zaitun.
30 Da suka rera waƙa, sai suka fita, suka tafi Dutsen Zaitun.
Da suka kusato Urushalima suka zo Betafaji, wajen Dutsen Zaitun, sai Yesu ya aiki almajiransa biyu,
Ina gaya muku, ba zan ƙara shan ruwan inabi ba, sai dai a ranar nan da za mu sha wani sabo tare da ku a Mulkin Ubana.”
Kullum da rana yakan koyar a Haikali, da dare kuma yakan fita ya kwana a dutsen da ake ce da shi Dutsen Zaitun.
“Bitrus, ya Bitrus, Shaiɗan ya nemi izinin sheƙe ku kamar alkama, ya kuwa samu.
Sai ya fita ya tafi Dutsen Zaitun, kamar yadda ya saba. Almajiransa kuwa suka bi shi.
sai dai domin duniya tă sani ina ƙaunar Uban, ina kuma yin yadda Uba ya umarce ni, ku tashi mu tafi daga nan.”