Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 26:27 - Littafi Mai Tsarki

27 Sai ya ɗauki ƙoƙo bayan ya kuma yi godiya ga Allah, sai ya ba su, ya ce, “Dukkanku ku shassha.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

27 Sa’an nan ya ɗauki kwaf, ya yi godiya, ya kuma ba su, yana cewa, “Ku shassha daga cikinsa, dukanku.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 26:27
12 Iomraidhean Croise  

Zan miƙa hadaya ta sha ga Ubangiji, Ina gode masa domin dā ya cece ni.


Na shiga cikin lambuna, budurwata, amaryata, Ina tattara mur da ƙaro. Ina shan zuma da kakinsa. Ina shan ruwan inabi da madara kuma. Ƙaunatattuna, ku ci ku sha, har ku bugu da ƙauna!


Bakinki kamar ruwan inabi mafi kyau ne. Idan haka ne bari ya bulbulo sosai zuwa ga ƙaunataccena, Ya gangara leɓunan masu barci.


A kan Dutsen Sihiyona Ubangiji Mai Runduna zai shirya wa dukan sauran al'umman duniya biki da abinci irin na adaras da ruwan inabi mafi kyau.


Ubangiji ya ce, “Duk mai jin ƙishi ya zo, Ga ruwa a nan! Ku da ba ku da kuɗi ku zo, Ku sayi hatsi ku ci! Ku zo ku sayi ruwan inabi da madara, Ba za ku biya kome ba!


Da ya ɗauki gurasa bakwai ɗin da kifayen nan, ya yi godiya ga Allah, sai ya gutsuttsura, ya yi ta ba almajiran, almajiran kuma na, bai wa jama'a.


Suna cikin cin abinci, sai Yesu ya ɗauki gurasa, ya yi godiya ga Allah, ya gutsuttsura, ya ba almajiran, ya ce, “Ungo, ku ci. Wannan jikina ne.”


Wannan jinina ne na tabbatar alkawari, wanda za a zubar saboda mutane da yawa, domin gafarar zunubansu.


Haka kuma, bayan jibi, ya ɗauki ƙoƙon, ya ce, “Ƙoƙon nan sabon alkawari ne, da aka tabbatar da jinina da za a bayar dominku.


Ƙoƙon nan na yin godiya, wanda muke gode wa Allah saboda shi, ashe, ba tarayya ne ga jinin Almasihu ba? Gurasar nan da muke gutsuttsurawa kuma, ashe, ba tarayya ce ga jikin Almasihu ba?


Sai dai kowa ya auna kansa, sa'an nan ya ci gurasar, ya kuma sha a ƙoƙon.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan