Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 26:26 - Littafi Mai Tsarki

26 Suna cikin cin abinci, sai Yesu ya ɗauki gurasa, ya yi godiya ga Allah, ya gutsuttsura, ya ba almajiran, ya ce, “Ungo, ku ci. Wannan jikina ne.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

26 Yayinda suke cikin cin abinci, Yesu ya ɗauki burodi, ya yi godiya ya kuma kakkarya, ya ba wa almajiransa yana cewa, “Ku karɓa ku ci; wannan jikina ne.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 26:26
16 Iomraidhean Croise  

Sa'an nan ya umarci taron su zazzauna a ɗanyar ciyawa. Da ya ɗauki gurasa biyar ɗin da kifi biyun, sai ya ɗaga kai sama, ya yi wa Allah godiya, ya gutsuttsura gurasar, ya yi ta ba almajiransa, almajiran kuma suna bai wa jama'a.


Sai ya ɗauki ƙoƙo bayan ya kuma yi godiya ga Allah, sai ya ba su, ya ce, “Dukkanku ku shassha.


Da ya ɗauki gurasa biyar ɗin da kifi biyun, sai ya ɗaga kai sama, ya yi wa Allah godiya, ya gutsuttsura gurasar, ya yi ta ba almajiran, suna kai wa jama'a, duk kuma ya raba musu kifin nan biyu.


Sai ya karɓi ƙoƙo, bayan da ya yi godiya ga Allah, ya ce, “Ungo wannan, ku shassha.


Sa'ad da yake cin abinci tare da su, sai ya ɗauki gurasa, ya yi wa Allah godiya, ya gutsura, ya ba su.


Kowace rana kuma sukan riƙa zuwa Haikali da nufi ɗaya, suna gutsuttsura gurasa a gidajensu, suna cin abinci da farin ciki ƙwarai, rai kwance,


A ranar farko ta mako kuma, da muka taru don gutsuttsura gurasa, Bulus ya yi masu jawabi, don ya yi niyyar tashi kashegari, sai ya yi ta jan jawabin nasa har tsakar dare.


duk kuma sun sha ruwan nan na ruhu. Domin sun sha ruwa daga Dutsen nan na ruhu, wanda ya yi tafiya tare da su. Dutsen nan kuwa Almasihu ne.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan