Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 26:25 - Littafi Mai Tsarki

25 Sai Yahuza da ya bashe shi ya ce, “Ko ni ne, ya Shugaba?” Yesu ya ce masa, “Ga shi, kai ma ka faɗa.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

25 Sa’an nan Yahuda, wanda zai bashe shi ya ce, “Tabbatacce ba ni ba ne, ko, Rabbi?” Yesu ya amsa ya ce, “I, kai ma ka fada.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 26:25
11 Iomraidhean Croise  

Sai ya shiga, ya tsaya a gaban Elisha, Elisha kuwa ya tambaye shi, “Ina ka tafi, Gehazi?” Sai ya ce, “Ranka ya daɗe ban tafi ko'ina ba.”


Ga yadda al'amarin mazinaciya yake, takan yi sha'aninta sa'an nan ta yi wanka ta ce, “Ban yi laifin kome ba!”


a gaishe su a kasuwa, a kuma riƙa ce da su ‘Malam’.


Amma ku kam, kada a ce muku ‘Malam’, domin Malaminku ɗaya ne, ku duka kuwa 'yan'uwa ne.


Sai ɗaya daga cikin sha biyun nan, mai suna Yahuza Iskariyoti, ya je wurin manyan firistoci,


Nan da nan ya matso wurin Yesu, ya ce, “Salama alaikun, ya Shugaba!” Sai ya yi ta sumbantarsa.


Sai Yesu ya ce masa, “Yadda ka faɗa. Ina kuwa gaya muku a nan gaba za ku ga Ɗan Mutum zaune a dama da Mai Iko, yana kuma zuwa a kan gajimare.”


To, sai Yesu ya tsaya a gaban mai mulki, mai mulkin kuma ya tambaye shi, “Ashe, kai ɗin nan kai ne Sarkin Yahudawa?” Yesu ya ce masa, “Yadda ka faɗa.”


Duk suka ce, “Ashe, kai ɗin nan Ɗan Allah ne?” Sai ya ce musu, “Yadda kuka faɗa, ni ne.”


Sai Bilatus ya ce masa, “Wato ashe, sarki ne kai?” Yesu ya amsa ya ce, “Yadda ka faɗa, ni sarki ne. Domin haka musamman aka haife ni, don haka kuma musamman na shigo duniya, domin in shaidi gaskiya. Kowane mai ƙaunar gaskiya kuwa yakan saurari muryata.”


Ana cikin haka sai almajiran suka roƙe shi suka ce, “Ya shugaba, ci abinci.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan