Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 26:24 - Littafi Mai Tsarki

24 Ɗan Mutum zai tafi ne, yadda labarinsa yake a rubuce, duk da haka kaiton mutumin nan da yake ba da Ɗan Mutum! Da ma ba a haifi mutumin nan ba, da zai fiye masa.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

24 Ɗan Mutum zai tafi kamar yadda aka rubuta game da shi. Amma kaiton mutumin da zai bashe Ɗan Mutum! Da ma ba a haifi mutumin nan ba, da ya fi masa.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 26:24
34 Iomraidhean Croise  

Zan sa ƙiyayya tsakaninka da matar, tsakanin zuriyarka da zuriyarta, shi zai ƙuje kanka, kai za ka ƙuje diddigensa.”


Allah ya sa mutuwa ta auko wa maƙiyana ba labari, Allah ya sa su gangara ƙasar matattu da ransu! Mugunta tana cikin gidajensu da zukatansu.


Amma kai, ya Allah, za ka jefar da masu kisankai, da maƙaryata can ƙasa cikin zurfafa, Kafin su kai rabin kwanakinsu a duniya. Amma ni, zan dogara gare ka.


Za ta kasance har shekara ɗari huɗu da talatin da huɗu, sa'an nan za a kashe Masihan, ba zai sami kome ba. Jama'ar shugaban da zai zo za su hallaka birnin da Haikali. A ƙarshensa za a yi rigyawa, da yaƙe-yaƙe, da hallakarwa kamar yadda aka ƙaddara.


“Zan cika zuriyar Dawuda da mutanen Urushalima da ruhun tausayi da na addu'a. Za su dubi wanda suka soke shi, har ya mutu. Za su yi makoki dominsa kamar waɗanda aka yi musu rasuwar ɗan farinsu.


“Ka farka, ya kai takobi, ka fāɗa wa makiyayina, Ka fāɗa wa mutumin da yake kusa da ni, Ka sari makiyayin domin tumakin su watse. Zan bugi ƙanana da hannuna, Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.


“Kaiton duniya saboda sanadodin tuntuɓe! Lalle sanadodin tuntuɓe ba su da makawa, duk da haka kaiton wanda shi ne sanadin!


Sai Yesu ya ce musu, “Duk za ku yi tuntuɓe sabili da ni a wannan dare domin a rubuce yake cewa, ‘Zan bugi makiyayi, tumakin garken kuwa za su fasu.’


To, ta yaya ke nan za a cika Littattafai a kan lalle wannan abu ya kasance?”


Amma duk wannan ya auku ne domin a cika littattafan annabawa.” Daga nan duk almajiran suka yashe shi, suka yi ta kansu.


Ga shi, Ɗan Mutum zai tafi ne, yadda labarinsa yake a rubuce, duk da haka kuwa, kaiton mutumin nan da yake ba da Ɗan Mutum! Da ma ba a haifi mutumin nan ba, da zai fiye masa.”


Sai ya ce musu, “Lalle ne Iliya ya fara zuwa ya raya dukan abubuwa. Yaya kuwa yake a rubuce a kan Ɗan Mutum, cewa zai sha wuya iri iri, a kuma wulaƙanta shi?


Lalle Ɗan Mutum zai ƙaura kamar yadda aka ƙaddara, duk da haka, kaiton mutumin nan da yake ba da shi!”


ya kuma ce musu, “Haka yake a rubuce, cewa wajibi ne Almasihu ya sha wuya, a rana ta uku kuma ya tashi daga matattu,


Duk sa'ad da nake tare da su, na kiyaye su da ikon sunanka da ka ba ni. Na kāre su, ba kuwa waninsu da ya halaka, sai dai halakakken nan, domin Nassi ya cika.


Sai suka ce wa juna, “Kada mu tsaga ta, sai dai mu yi kuri'a a kanta, mu ga wanda zai ci.” Wannan kuwa domin a cika Nassi ne cewa, “Sun raba tufafina a junansu. Taguwata kuwa suka jefa kuria akanta.”


Bayan haka, Yesu da ya san duk an gama kome, domin a cika Nassi sai ya ce, “Ina jin ƙishirwa.”


shi Yesun nan fa, an ba da shi bisa ƙaddarar Allah da rigyasaninsa, ku kuwa kuka gicciye shi, kuka kashe shi, ta hannun masu zunubi.


Da suka sa masa rana, sai suka zo masaukinsa, su da yawa. Sa'an nan ya yi ta yi musu bayani, yana ta shaidar musu Mulkin Allah, tun daga safe har magariba, yana ƙoƙarin rinjayarsu a kan Yesu, ta hanyar Attaurar Musa da littattafan annabawa.


Sun haɗa kai domin su yi dukan abin da ka ƙaddara zai auku, bisa ga ikonka da nufinka.


Jawabi mafi muhimmanci da na sanar da ku, shi ne wanda na karɓo, cewa, Almasihu ya mutu domin zunubanmu, kamar yadda Littattafai suka faɗa,


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan