23 Sai ya amsa ya ce, “Wanda muke ci a ƙwarya ɗaya, shi ne zai bashe ni.
23 Yesu ya amsa ya ce, “Wanda ya sa hannunsa a kwano tare da ni ne, zai bashe ni.
Har da shaƙiƙin abokina, Wanda na fi amincewa da shi. Wanda muke ci tare, ya juya yana gāba da ni.
Waɗansu mutane sun cika lalaci, ko abincinsu ba su iya taunawa.
Sai suka yi baƙin ciki gaya, suka fara ce masa da ɗaya ɗaya, “Ni ne, ya Ubangiji?”
Amma ga shi, mai bashe ni ɗin nan yana ci a akushi ɗaya da ni.
Ba dukanku nake nufi ba. Na san waɗanda na zaɓa. Wannan kuwa duk domin a cika Nassi ne cewa, ‘Wanda yake cin abincina ya tasar mini.’