Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 26:18 - Littafi Mai Tsarki

18 Sai ya ce, “Ku shiga gari wurin wāne, ku ce masa, ‘Malam ya ce lokacinsa ya yi kusa, zai ci Idin Ƙetarewa a gidanka tare da almajiransa.’ ”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

18 Ya amsa ya ce, “Ku shiga gari wurin wāne, ku ce masa, ‘Malam ya ce, lokacina ya yi kusa. Zan ci Bikin Ƙetarewa tare da almajiraina a gidanka.’ ”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 26:18
18 Iomraidhean Croise  

Kowa ya yi muku magana, ku ce, ‘Ubangiji ne yake bukatarsu,’ zai kuwa aiko da su nan da nan.”


Kada kuma a kira ku ‘Shugabanni’, domin Shugaba ɗaya gare ku, wato, Almasihu.


Amma ku kam, kada a ce muku ‘Malam’, domin Malaminku ɗaya ne, ku duka kuwa 'yan'uwa ne.


Almajiran kuwa suka yi yadda Yesu ya umarce su, suka shirya Idin Ƙetarewa.


“Kun san Idin Ƙetarewa saura kwana biyu, za a kuma ba da Ɗan Mutum a gicciye shi.”


Nan da nan ya matso wurin Yesu, ya ce, “Salama alaikun, ya Shugaba!” Sai ya yi ta sumbantarsa.


Yana cikin magana, sai ga waɗansu daga gidan shugaban majami'a suka ce, “Ai, 'yarka ta rasu, me kuma za ka wahalar da Malamin?”


Sa'ad da nake tare da ku kowace rana a cikin Haikali, ba ku miƙa hannu garin ku kama ni ba. Amma wannan lokacinku ne da na ikon duhu.”


Da ta faɗi haka, ta je ta kirawo 'yar'uwa tata Maryamu, ta raɗa mata ta ce, “Ga Malam ya zo, yana kiranki.”


Yesu ya amsa musu ya ce, “Lokaci ya yi da za a ɗaukaka Ɗan Mutum.


Ana nan tun kafin Idin Ƙetarewa, da Yesu ya san lokacinsa ya yi da zai tashi daga wannan duniya ya koma wurin Uba, da yake ya ƙaunaci mutanensa da suke duniya, ya ƙaunace su har matuƙa.


Da Yesu ya faɗi haka, sai ya ɗaga kai sama ya ce, “Ya Uba, lokaci ya yi. Ka ɗaukaka Ɗanka domin Ɗan ya ɗaukaka ka,


Yesu ya ce mata, “Maryamu!” Sai ta juya ta ce masa da Yahudanci, “Rabboni!” wato Malam.


Don haka suka nema su kama shi, amma ba wanda ya taɓa shi, domin lokacinsa bai yi ba tukuna.


Sai Yesu ya ce musu, “Lokacina bai yi ba tukuna, amma ku, koyaushe lokacinku ne.


Ku dai ku tafi idin. Ni ba za ni ba yanzu, don lokacina bai yi sosai ba tukuna.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan