Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 26:13 - Littafi Mai Tsarki

13 Hakika, ina gaya muku, duk inda za a yi bisharar nan a duniya duka, abin da matar nan ta yi za a riƙa faɗarsa don tunawa da ita.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

13 Gaskiya nake gaya muku, duk inda aka yi wa’azin bisharan nan a duniya duka, abin da matan nan ta yi, za a riƙa faɗarsa don tunawa da ita.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 26:13
19 Iomraidhean Croise  

Mutumin kirki ba zai kāsa ba daɗai, Ba za a taɓa mantawa da shi ba.


Ku ɓarke da sowar murna, Ku kufan Urushalima! Ubangiji ya ta'azantar da jama'arsa, Ya fanshi birninsa.


Za a kuma yi bisharar nan ta Mulkin Sama ko'ina a duniya domin shaida ga dukkan al'ummai. Sa'an nan kuma sai ƙarshen ya zo.”


Don haka sai ku je ku almajirtar da dukkan al'ummai, kuna yi musu baftisma da sunan Uba, da Ɗa, da Ruhu Mai Tsarki,


Amma lalle sai an fara yi wa dukan al'ummai bishara.


Hakika kuwa ina gaya muku, duk inda za a yi bishara a duniya duka, abin da matan nan ta yi, za a riƙa faɗarsa domin tunawa da ita.”


Sai ya ce musu, “Ku tafi ko'ina a duniya, ku yi wa dukkan 'yan adam bishara.


a kuma yi wa dukan al'ummai wa'azi su tuba, a gafarta musu zunubansu saboda sunansa. Za a kuwa fara daga Urushalima.


Shi kuwa ya zura masa ido a tsorace, ya ce, “Ya Ubangiji, mene ne?” Mala'ikan kuma ya ce masa, “Addu'arka da sadakarka sun kai har a gaban Allah, abubuwan tunawa ne kuma a gare shi.


Amma ina tambaya. Ba su ji jawabin ba ne? Hakika sun ji. “Muryarsu ta gama duniya duka, Maganarsu kuma ta kai har bangon duniya.”


ta wurin ikon mu'ujizai, da abubuwan al'ajabai, da kuma ta wurin ikon Ruhun, har dai daga Urushalima da kewayenta, har zuwa Ilirikun, na yi bisharar Almasihu a ko'ina.


Ai, ba mai yabon kansa ake yarda da shi ba, sai dai wanda Ubangiji ya yaba wa.


Sai dai fa ku nace wa bangaskiya, zaunannu, kafaffu, ba tare da wata ƙaura daga begen nan na bishara wadda kuka ji ba, wadda aka yi wa dukkan talikan da suke a duniya, wadda kuma ni Bulus na zama mai hidimarta.


wato, bisharar da ta zo muku, kamar yadda ta zo wa duniya duka, tana hayayyafa, tana kuma ƙara yaɗuwa, kamar yadda take yi a tsakaninku tun daga ranar da kuka ji, kuka kuma fahimci alherin Allah na hakika.


wanda ya ba da kansa fansa saboda kowa da kowa. An kuwa yi shaidar wannan a daidai lokacinsa.


Gama Allah ba marar adalci ba ne, har da zai ƙi kula da aikinku, da kuma ƙaunar sunansa da kuka yi, wajen yi wa tsarkaka hidima, har yanzu ma kuna yi.


Sa'an nan na ga wani mala'ika yana kaɗawa a tsakiyar sararin sama, yana tafe da madawwamiyar bishara, domin ya sanar da ita ga mazaunan duniya, wato, ga kowace al'umma, da kabila, da harshe, da jama'a.


Ni Ubangiji Allah na Isra'ila, na yi alkawari a dā cewa, ‘Kai da iyalinka da danginka za ku yi mini aikin firist har abada.’ Amma yanzu na ce ba zan yarda da wannan ba. Waɗanda suke girmama ni, zan girmama su. Waɗanda suke raina ni zan ƙasƙantar da su ƙwarai.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan