Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 26:11 - Littafi Mai Tsarki

11 Kullum kuna tare da talakawa, amma ba kullum ne kuke tare da ni ba.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

11 Matalauta za su kasance tare da ku kullum, amma ni ba zan kasance tare da ku kullum ba.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 26:11
16 Iomraidhean Croise  

Gama kuwa inda mutum biyu ko uku suka taru saboda sunana, ni ma ina nan a tsakiyarsu.”


Yesu kuwa da ya lura da haka, sai ya ce musu, “Don me kuke damun matar nan? Ai, alheri ta yi mini, na gaske kuwa.


kuna koya musu su kiyaye duk iyakar abin da na umarce ku. Ga shi, ni kuma kullum ina tare da ku har zuwa matuƙar zamani.”


Kullum kuna tare da gajiyayyu, ko yaushe kuma kuke so, kwa iya yi musu alheri, amma ba kullum ne kuke tare da ni ba.


Ai, kullum kuna tare da gajiyayyu, amma ba kullum kuke tare da ni ba.”


Ya ku 'ya'yana ƙanana, saura ɗan lokaci kaɗan ina tare da ku. Za ku neme ni, amma kamar yadda na faɗa wa Yahudawa cewa, ‘Inda za ni ba za ku iya zuwa ba,’ haka nake faɗa muku yanzu.


Saura ɗan lokaci kaɗan duniya ba za ta ƙara ganina ba, amma ku za ku gan ni. Saboda ni a raye nake, ku ma za ku rayu.


Daga wurin Uban ne na fito, na shigo duniya, har wa yau kuma zan bar duniya in koma wurin Uba.”


Yanzu kuwa za ni wurin wanda ya aiko ni, duk da haka a cikinku, ba wanda ya tambaye ni, ‘Ina za ka?’


Yanzu kuma ba sauran zamana a duniya, amma waɗannan a duniya suke, ni kuwa ina zuwa wurinka. Ya Uba Mai tsarki, ka kiyaye su da ikon sunanka da ka ba ni, su zama ɗaya kamar yadda muke.


wanda lalle ne ya zauna a Sama, har kafin lokacin nan na sabunta dukkan abubuwa da Allah ya faɗa tun zamanin dā ta bakin annabawansa tsarkaka.


Sai dai kuma suna so mu tuna matalauta, wannan kuwa ko dā ma ina da himmar yi ƙwarai.


Gama ba za a rasa matalauta a ƙasar ba, saboda haka nake umartarku, cewa ku zama da hannu sake ga 'yan'uwanku, da mabukaci, da matalauci.”


Duk kuwa wanda yake da abin hannunsa, yake kuma ganin ɗan'uwansa da rashi, sa'an nan ya rufe ido gare shi, ƙaƙa ƙaunar Allah yake zaune a cikinsa?


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan