Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 26:10 - Littafi Mai Tsarki

10 Yesu kuwa da ya lura da haka, sai ya ce musu, “Don me kuke damun matar nan? Ai, alheri ta yi mini, na gaske kuwa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

10 Sane da wannan, Yesu ya ce musu, “Me ya sa kuke damun macen nan? Ta yi mini abu mai kyau ne.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 26:10
24 Iomraidhean Croise  

Na kuma faɗa musu yadda Allah yana tare da ni, ya kuma taimake ni, da maganar da sarki ya faɗa mini. Sai suka ce, “Mu tashi, mu kama gini.” Suka himmatu su yi wannan aiki nagari.


Me ya sa kuke yin ƙarya? Kuna tsammani ƙarairayinku za su taimaki Allah?


Kullum kuna tare da talakawa, amma ba kullum ne kuke tare da ni ba.


Da ma an sayar da man nan kuɗi mai yawa, an ba gajiyayyu!”


Amma Yesu ya ce, “Ku ƙyale ta. Don me kuke damunta? Ai, alheri ta yi mini, na gaske kuwa.


Yana cikin magana, sai ga wani ya zo daga gidan shugaban majami'ar, ya ce, “Ai, 'yarka ta rasu. Kada ka ƙara wahalar da Malamin.”


Allah kuwa yana da iko yă ba ku fiye da bukatarku, domin kullum ku wadata da kome ta kowace hanya, kuna ta bayarwa hannu sake, kowane irin kyakkyawan aiki.


alhali kuwa ba wata bishara dabam, sai dai akwai waɗansu da suke ta da hankalinku, suna son jirkitar da bisharar Almasihu.


Da ma a ce masu ta da hankalinku ɗin nan su mai da kansu babanni!


Daga nan gaba kada kowa ya ƙara damuna, domin a jikina ina da tabbai masu nuna ni bawan Ubangiji Yesu ne.


Ai, mu aikinsa ne, an sāke halittarmu a cikin Almasihu Yesu musamman domin mu yi kyawawan ayyuka, waɗanda Allah ya tanadar mana tun da fari, mu yi.


domin ku yi zaman da ya cancanci bautar Ubangiji, kuna faranta masa ta kowane fanni, kuna ba da amfani a kowane aiki nagari, kuna ƙaruwa da sanin Allah.


yă ta'azantar da ku, ya kuma ƙarfafa ku ga yin kowane kyakkyawan aiki da magana.


Maganar nan tabbatacciya ce, cewa duk mai burin aikin kula da ikkilisiya, yana burin yin aiki mai kyau ke nan.


wadda ake yabo a kan kyawawan ayyukanta, wadda kuma ta goyi 'ya'ya sosai, ta yi wa baƙi karamci, ta wanke ƙafafun tsarkaka, ta taimaki ƙuntatattu, ta kuma nace wa yin kowane irin aiki nagari.


Kowa yă tsarkake kansa daga ayyukan nan ƙasƙantattu, zai zama ma'aikaci mai daraja, tsarkakakke, mai amfani ga Ubangiji, shiryayye ga kowane kyakkyawan aiki.


Suna cewa sun san Allah, amma suna sāɓa masa ta wurin aikinsu. Abin ƙyama ne su, kangararru, ko kaɗan ba su da wani amfani a wajen yin aiki nagari.


wanda ya ba da kansa dominmu, domin ya fanso mu daga dukan mugun aiki, ya kuma tsarkake jama'a su zama abin mulkinsa, masu himmar yin kyakkyawan aiki.


Ka riƙa tuna musu su yi wa mahukunta da shugabanni ladabi, suna yi musu biyayya, suna kuma zaune da shirinsu na yin kowane irin kyakkyawan aiki.


Jama'armu su koyi himmantuwa ga aikin kirki don biyan bukatun matsattsu, kada su zama marasa amfani.


Maganar nan tabbatacciya ce. Ina so ka ƙarfafa waɗannan abubuwa ƙwarai, don waɗanda suka ba da gaskiya ga Allah su himmantu ga aiki nagari, waɗannan abubuwa kuwa masu kyau ne, masu amfani kuma ga mutane.


yă kamala ku da kowane irin kyakkyawan abu, domin ku aikata nufinsa, yă kuma aikata a cikinmu abin da yake faranta masa rai ta wurin Yesu Almasihu. Ɗaukaka tā tabbata a gare shi har abada abadin. Amin, Amin.


Ku yi halin yabo a cikin al'ummai, don duk sa'ad da suke kushenku, cewa ku mugaye ne, sai su ga kyawawan ayyukanku, har su ɗaukaka Allah a ran da alheri ya sauko musu.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan