Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 25:44 - Littafi Mai Tsarki

44 Sa'an nan su ma za su amsa su ce, ‘Ya Ubangiji, a yaushe muka gan ka da yunwa, ko da ƙishirwa, ko da baƙunci, ko da huntanci, ko da rashin lafiya, ko a kurkuku, ba mu kula da kai ba?’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

44 “Su ma za su amsa, su ce, ‘Ubangiji, yaushe muka gan ka cikin yunwa ko ƙishirwa ko baƙo ko cikin bukatar tufafi ko cikin rashin lafiya ko cikin kurkuku, ba mu taimake ka ba?’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 25:44
14 Iomraidhean Croise  

Ƙaƙa za ka ce ba ka ƙazantar da kanka ba, Ba ka taɓa bin gunkin nan Ba'al ba? Ka duba hanyarka ta zuwa cikin kwari, ka san abin da ka yi. Kana kama da taguwa, mai yawon neman barbara.


‘Ba mu da laifi, hakika kuwa, Ubangiji bai yi fushi da mu ba.’ Amma ni Ubangiji zan hukunta ku, Domin kun ce ba ku yi zunubi ba.


Ubangiji Mai Runduna ya ce wa firistoci, “Ɗa yakan girmama mahaifinsa, bara kuwa yakan girmama maigidansa. Ni Ubanku ne, me ya sa ba ku girmama ni ba? Ni kuma Maigidanku ne, me ya sa ba ku ganin darajata? Kun raina ni, duk da haka kuna tambaya cewa, ‘Ƙaƙa muka raina ka?’


Kun gajiyar da Ubangiji Mai Runduna da maganganunku, amma kun ce, “Ƙaƙa muka gajiyar da shi?” Kuna cewa, “Ubangiji yana ganinsu, dukan masu aikata mugunta mutanen kirki ne, yana kuwa ƙaunarsu.” Kuna kuma cewa, “Ina Allah yake wanda yake shi adali ne?”


“Kun faɗi mugun abu a kaina,” in ji Ubangiji, “Amma kun ce, ‘Me muka ce a kanka?’


Wanda ya yi na'am da wani annabi domin shi annabi ne, zai sami ladar annabi. Wanda kuma ya yi na'am da adali domin shi adali ne, zai sami ladar adali.


Na yi baƙunci, ba ku sauke ni ba. Na yi huntanci, ba ku tufasar da ni ba. Na yi rashin lafiya, ina kuma kurkuku, ba ku kula da ni ba.’


Sa'an nan zai amsa musu ya ce, ‘Hakika, ina gaya muku, tun da yake ba ku yi wa ɗaya daga cikin waɗannan mafi ƙanƙanta ba, ai, ni ne ba ku yi mini ba.’


“Albarka tā tabbata ga masu kwaɗaita ga adalci, domin za a biya musu muradi.


A ranar nan da yawa za su ce mini, ‘Ya Ubangiji, ya Ubangiji, ashe, ba mu yi annabci da sunanka ba? Ba mu fitar da aljannu da sunanka ba? Ba mu kuma yi ayyukan al'ajabi masu yawa da sunanka ba?’


Shi kuwa mutumin, don yana son baratar da kansa, ya ce wa Yesu, “To, wane ne ɗan'uwa nawa?”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan