Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 25:40 - Littafi Mai Tsarki

40 Sai Sarkin zai amsa musu ya ce, ‘Hakika, ina gaya muku, tun da yake kun yi wa ɗaya daga cikin waɗannan 'yan'uwana mafi ƙanƙanta, ai, ni kuka yi wa.’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

40 “Sarkin zai amsa ya ce, ‘Gaskiya nake gaya muku, duk abin da kuka yi wa ɗaya daga cikin waɗannan ’yan’uwana mafi ƙanƙanta, ni kuka yi wa.’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 25:40
42 Iomraidhean Croise  

Dawuda ya yi tambaya, ko akwai wani da ya ragu daga gidan Saul, wanda zai nuna wa alheri saboda Jonatan.


Dawuda ya ce masa, “Kada ka ji tsoro, gama zan yi maka alheri ne saboda mahaifinka, Jonatan. Zan mayar maka da dukan gonakin kakanka, Saul. Kullum kuma za ka riƙa cin abinci a teburina.”


Bari mu gina masa ɗan ɗaki a kan bene, mu sa masa gado, da tebur, da kujera, da fitila, don duk sa'ad da ya zo ya sauka a wurin.”


Wanda ya zalunci matalauci ya zargi Mahaliccinsa ke nan, amma nuna alheri ga matalauci yin sujada ne.


Sa'ad da ka bayar ga matalauci kamar ka ba Ubangiji rance ne, gama Ubangiji zai sāka maka.


Amma a ranan nan, ni Ubangiji zan cece ka, ba za a ba da kai a hannun mutanen da kake jin tsoronsu ba.


“Wanda ya yi na'am da ku, ya yi na'am da ni ke nan. Wanda ya yi na'am da ni kuwa, to, ya yi na'am da wanda ya aiko ni.


Kowa ya ba ɗaya daga cikin 'yan yaran nan, ko da moɗa guda ta baƙin ruwa, kan shi almajirina ne, hakika, ina gaya muku, ba zai rasa ladarsa ba.”


“Ku dai lura, kada ku raina ɗaya daga cikin waɗannan 'yan yara. Ina gaya muku, mala'ikunsu a Sama kullum suna duban fuskar Ubana da yake cikin Sama.


Sa'an nan ne Sarki zai ce wa waɗanda suke dama da shi, ‘Ku zo, ya ku da Ubana ya yi wa albarka, sai ku gāji mulkin da aka tanadar muku tun daga farkon duniya.


Ko kuma a yaushe muka gan ka da rashin lafiya, ko a kurkuku muka kula da kai?’


Sa'an nan zai amsa musu ya ce, ‘Hakika, ina gaya muku, tun da yake ba ku yi wa ɗaya daga cikin waɗannan mafi ƙanƙanta ba, ai, ni ne ba ku yi mini ba.’


Sai Yesu ya ce musu, “Kada ku ji tsoro, ku je ku gaya wa 'yan'uwana su tafi ƙasar Galili, a can ne za su gan ni.”


Kowa kuma ya ba ku ruwan sha moɗa guda saboda ku na Almasihu ne, hakika ina gaya muku, ba zai rasa ladansa ba ko kaɗan.


Suka ce, “Albarka ta tabbata ga Sarkin nan mai zuwa da sunan Ubangiji! Salama ta tabbata a Sama, ɗaukaka kuma ga Allah!”


Yesu ya ce mata, “Kada ki riƙe ni, domin har yanzu ban hau wurin Uba ba tukuna. Sai dai ki tafi wurin 'yan'uwana ki ce musu ina hawa wurin Ubana kuma Ubanku, Allahna kuma Allahnku.”


Waɗanda Allah ya riga ya zaɓa tun tuni, su ne ya ƙaddara su ɗauki kamannin Ɗansa, domin shi Ɗan yă zama na farko a cikin 'yan'uwa masu yawa.


Domin ba wa'azin kanmu muke yi ba, sai dai na Yesu Almasihu a kan shi ne Ubangiji, mu kuwa bayinku ne saboda Yesu.


Ya ku 'yan'uwa, don 'yanci musamman aka kira ku, amma kada ku mai da 'yancin nan naku hujjar biye wa halin mutuntaka, sai dai ku bauta wa juna da ƙauna.


Albarkar Ruhu kuwa ita ce ƙauna, da farin ciki, da salama, da haƙuri, da kirki, da nagarta, da aminci,


In muna a cikin Almasihu Yesu, kaciya da rashin kaciya ba a bakin kome suke ba. Bangaskiya mai aikata ƙauna ita ce wani abu.


domin mu gaɓoɓin jikinsa ne.


Gama Allah ba marar adalci ba ne, har da zai ƙi kula da aikinku, da kuma ƙaunar sunansa da kuka yi, wajen yi wa tsarkaka hidima, har yanzu ma kuna yi.


Da yake kun tsarkake ranku kuna yi wa gaskiya biyayya har kuna nuna sahihiyar ƙauna ga 'yan'uwa, sai ku himmantu ga ƙaunar juna da zuciya ɗaya.


Kowa ya ce yana ƙaunar Allah, alhali kuwa yana ƙin dan'uwansa, to, maƙaryaci ne. Don wanda ba ya ƙaunar ɗan'uwansa da yake gani, ba dama ya ƙaunaci Allah wanda bai taɓa gani ba.


Za su yi yaƙi da Ɗan Ragon, Ɗan Ragon kuwa zai cinye su, shi da waɗanda suke tare da shi, kirayayyu, zaɓaɓɓu, amintattu, domin shi ne Ubangijin iyayengiji.”


Da wani suna a rubuce a jikin rigarsa, har daidai cinyarsa, wato Sarkin sarakuna, Ubangijin iyayengiji.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan