Kana ƙaunar abin da yake daidai, Kana ƙin abin da yake mugu. Saboda haka Allah, Allahnka, ya zaɓe ka, Ya kuwa kwararo maka farin ciki mai yawa fiye da kowa.
Amma ku kam, ba masu zaman halin mutuntaka ba ne, masu zaman Ruhu ne, in dai har Ruhun Allah yana zaune a zuciyarku. Duk wanda ba shi da Ruhun Almasihu kuwa, ba na Almasihu ba ne.
Ku kam, shafar nan da kuka samu daga Ruhu Mai Tsarki tā tabbata a zuciyarku, ba sai wani ya koya muku ba. Amma kamar yadda shafar nan tasa take koya muku kome, ita kuwa gaskiya ce ba ƙarya ba, yadda dai ta koya muku, to, sai ku zauna a cikinsa.