Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 25:32 - Littafi Mai Tsarki

32 Za a tara dukan al'ummai a gabansa, zai kuma ware su dabam dabam, kamar yadda makiyayi yake ware tumaki da awaki.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

32 Za a tara dukan al’ummai a gabansa, zai kuma raba mutane dabam-dabam yadda makiyayi yakan ware tumaki daga awaki.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 25:32
22 Iomraidhean Croise  

Allah kuwa zai hukunta mugaye, Masu zunubi kuwa za a ware su daga adalai.


Sa'an nan ya bi da jama'arsa Kamar makiyayi, ya fito da su, Ya yi musu jagora cikin hamada.


A gaban Ubangiji, gama ya zo ne ya mallaki duniya. Zai mallaki dukan jama'ar duniya Da adalci da gaskiya.


A gaban Ubangiji, gama ya zo ne ya yi mulki bisa duniya! Zai yi mulki bisa dukan jama'ar duniya da adalci da gaskiya.


Zan fitar da 'yan tawaye a cikinku, da waɗanda suke yin mini laifi. Zan fito da su daga ƙasar da suke zaune, amma ba za su shiga ƙasar Isra'ila ba. Za ku kuwa sani ni ne Ubangiji Allah.


Sa'an nan za ku ga bambanci tsakanin masu adalci da mugaye, da tsakanin mutumin da yake bauta mini da wanda ba ya bauta mini.”


Haka zai kasance a ƙarshen duniya. Mala'iku za su fito, su ware mugaye daga masu adalci,


Don haka sai ku je ku almajirtar da dukkan al'ummai, kuna yi musu baftisma da sunan Uba, da Ɗa, da Ruhu Mai Tsarki,


Ƙwaryar shiƙarsa na hannunsa, zai kuwa share masussukarsa sarai sarai, ya taro alkamarsa ya sa a rumbunsa, amma ɓuntun, sai ya ƙone a wutar marar kasuwa.”


Ni ne Makiyayi mai kyau. Na san nawa, nawa kuma sun san ni,


Tumakin nan nawa sukan saurari muryata, na san su, suna kuma bi na.


Ɗaukacin waɗanda suka yi zunubi a rashin sanin Shari'a, za su hallaka ne ba tare da Shari'a ba. Ɗaukacin waɗanda suka yi zunubi a ƙarƙashin Shari'a kuwa, za a hukunta su ta hanyar Shari'a.


A wannan rana Allah zai yi wa 'yan adam shari'a a kan asiransu, ta wurin Yesu Almasihu, bisa ga bishara da nake wa'azinta.


Don haka, kada ku yanke wani hukunci tun lokaci bai yi ba, kafin komowar Ubangiji, wanda zai tone al'amuran da suke ɓoye a duhu, ya kuma bayyana nufin zukata. A sa'an nan ne, Allah zai yaɓa wa kowa daidai gwargwado.


Don lalle ne a gabatar da mu duka, a gaban kursiyin shari'a na Almasihu, domin kowa yă sami sakamakon abin da ya yi tun yana tare da wannan jiki, ko mai kyau ne, ko kuma marar kyau.


Za a hallakar da maƙiyan Ubangiji, Zai yi musu tsawa daga Sama. Ubangiji zai hukunta dukan duniya, Zai ba sarkinsa iko, Zai sa zaɓaɓɓen sarkinsa ya zama mai nasara.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan