Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 25:30 - Littafi Mai Tsarki

30 Ku kuma jefa banzan bawan nan a baƙin duhu. Nan za a yi kuka da cizon baki.’ ”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

30 Ku jefar da banzan bawan nan waje, cikin duhu, inda za a yi kuka da cizon haƙora.’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 25:30
19 Iomraidhean Croise  

Sa'ad da mugaye suka ga wannan, Sai suka tunzura, suka harare shi da fushi, suka ɓace, Sa zuciyarsu ta ƙare har abada.


su kuma jefa su cikin wuta mai ruruwa. Nan za su yi kuka da cizon haƙora.


su jefa su cikin wuta mai ruruwa. Nan za su yi kuka da cizon hakora.”


Sai sarki ya ce wa barorinsa, ‘Ku ɗaure shi ƙafa da hannu, ku jefa shi cikin matsanancin duhu. Nan za a yi kuka da cizon baƙi.’


yă farfasa masa jiki da bulala, ya ba shi rabonsa tare da munafukai. Nan za a yi kuka da cizon baki.”


Koyanzu ma an ɗora bakin gatari a gindin bishiya. Saboda haka duk bishiyar da bata bada 'ya'ya masu kyau ba, sai a sare ta a jefa a wuta.


“Ku ne gishirin duniya. Amma in gishiri ya sāne, da me za a daɗaɗa shi? Ba shi da sauran amfani, sai dai a zubar, mutane kuma su tattake.


'ya'yan Mulki kuwa sai a jefa su matsanancin duhu. Nan za su yi kuka da cizon haƙora.”


Sa'ad da kuka ga Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, da dukan annabawa a Mulkin Allah, ku kuwa ana korarku, a nan ne za ku yi kuka da cizon baki.


Duk wanda bai zauna a cikina ba, za a yar da shi can, kamar reshe, yă bushe, a kuma tattara irinsu a jefa wuta, a ƙone.


Jama'armu su koyi himmantuwa ga aikin kirki don biyan bukatun matsattsu, kada su zama marasa amfani.


Mutanen nan kamar mabubbugen ruwa wadanda suka kafe, ƙasashi ne da iska take kaɗawa. Su ne aka tanada wa matsanancin duhu.


Su kamar raƙuman ruwan teku ne masu hauka, suna taƙama da kumfar kunyarsu. Su kamar taurari ne masu kai da kawowa, waɗanda aka tanada wa matsanancin duhu har abada.


Amma matsorata, da marasa riƙon amana, da masu aikin ƙyama, da masu kisankai, da fasikai, da masu sihiri, da masu bautar gumaka, da kuma duk maƙaryata, duk rabonsu tafkin nan ne mai cin wuta da kibiritu, wanda yake shi ne mutuwa ta biyu.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan