Duk da haka suna ta nemana kowace rana, suna murna su san al'amurana, sai ka ce su al'umma ce wadda take aikata adalci, wadda kuma ba ta rabu da dokokin Allahnta ba. Suna roƙona in yi musu shari'ar adalci, suna murna su zo kusa da Allah.”
“Ka kuma rubuta wa mala'ikan ikkilisiyar da take a Sardisu haka, ‘Ga maganar mai Ruhohin Allah guda bakwai, da kuma taurarin nan bakwai. “ ‘Na san ayyukanka, kai rayayye ne, alhali kuwa matacce ne kai.