Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 25:21 - Littafi Mai Tsarki

21 Sai ubangijinsa ya ce masa, ‘Madalla, bawan kirki, mai aminci. Kā yi gaskiya a kan ƙaramin abu, zan ɗora ka a kan mai yawa. Ka zo ku yi farin ciki tare da ubangidanka.’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

21 “Maigidansa ya amsa ya ce, ‘Madalla, bawan kirki mai aminci! Ka yi aminci a kan abubuwa kaɗan, zan sa ka lura da abubuwa masu yawa. Zo ka yi farin ciki tare da maigidanka!’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 25:21
30 Iomraidhean Croise  

Sarakuna suna jin daɗin ƙwararrun 'yan majalisarsu, amma sukan hukunta waɗanda suka ba su kunya.


Amintaccen mutum zai cika kwanakinsa lafiya, amma idan kana so ka sami dukiya dare ɗaya, za a hukunta ka.


“Wane ne amintaccen bawan nan mai hikima, da ubangidansa ya ba shi riƙon gidansa, yă riƙa ba su abincinsu a kan kari?


Hakika, ina gaya muku, sai ya ɗora shi a kan dukan mallakarsa.


Sai ubangijinsa ya ce masa, ‘Madalla, bawan kirki, mai aminci. Kā yi gaskiya a kan ƙaramin abu, zan ɗora ka a kan mai yawa. Ka zo ku yi farin ciki tare da ubangijinka.’


Waɗannan ne za su shiga madawwamiyar azaba, masu adalci kuwa rai madawwami.”


Hakika, ina gaya muku, sai ya ɗora shi a kan dukan mallaka tasa.


“Wanda yake da aminci a ƙaramin abu, mai aminci ne a babban abu. Wanda yake marar gaskiya a ƙaramin abu, marar gaskiya ne a babban abu.


Wanda duk zai bauta mini, ya bi ni. Inda nake kuma, nan bawana zai kasance shi ma. Kowa yake bauta mini, Uba zai girmama shi.”


In kuwa na je na shirya muku wuri, sai in dawo in kai ku wurina, domin inda nake, ku ma ku zama kuna can.


Ya Uba, ina so waɗanda ka ba ni, su ma su kasance tare da ni inda nake, su dubi ɗaukakata da ka yi mini, domin ka ƙaunace ni tun ba a halicci duniya ba.


Wanda yake Bayahude a zuci, ai, shi ne Bayahude. Kaciyar ainihi kuwa a zuci take, wato ta ruhu, ba ta zahiri ba. Irin wannan mutum, Allah ne yake yaba masa, ba ɗan adam ba.


Don haka, kada ku yanke wani hukunci tun lokaci bai yi ba, kafin komowar Ubangiji, wanda zai tone al'amuran da suke ɓoye a duhu, ya kuma bayyana nufin zukata. A sa'an nan ne, Allah zai yaɓa wa kowa daidai gwargwado.


Ai, ba mai yabon kansa ake yarda da shi ba, sai dai wanda Ubangiji ya yaba wa.


Saboda haka, ko muna gunsa, ko muna a rabe da shi, burinmu shi ne mu faranta masa zuciya.


Duka biyu suna jan hankalina ƙwarai. Burina in ƙaura in zauna tare da Almasihu, domin wannan shi ne ya fi kyau nesa.


Masu hidimar da suke aikinsu sosai, suna samar wa kansu kyakkyawan suna, da kuma ƙaƙƙarfar amincewa ga bangaskiyarsu ga Almasihu Yesu.


In mun jure, za mu yi mulki ma tare da shi, In mun yi musun saninsa, shi ma zai yi musun saninmu,


muna zuba ido ga Yesu, shi da yake shugaban bangaskiyarmu, da kuma mai kammala ta, wanda domin farin cikin da aka sa a gabansa ya daure wa gicciye, bai mai da shi wani abin kunya ba, a yanzu kuma a zaune yake a dama ga kursiyin Allah.


Kada ka ji tsoron wuyar da za ka sha. Ga shi, Iblis yana shiri ya jefa waɗansunku a kurkuku don a gwada ku, za ku kuwa sha tsanani har kwana goma. Ka riƙi amana ko da za a kashe ka, ni kuwa zan ba ka kambin rai.


Duk wanda ya ci nasara, zai ci wannan gādo, wato, in zama Allahnsa, shi kuma ya zama ɗa a gare ni.


Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi izinin zama tare da ni a kursiyina. kamar yadda ni ma na ci nasara, na kuma zauna tare da Ubana a kursiyinsa.


domin Ɗan Ragon nan da yake a tsakiyar kursiyin, shi zai zama makiyayinsu, zai kuwa kai su maɓuɓɓugar ruwan rai. Allah kuma zai share musu dukan hawaye.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan