Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 25:15 - Littafi Mai Tsarki

15 Ya ba ɗaya talanti biyar, ɗaya talanti biyu, wani kuma ya ba shi ɗaya, kowa dai gwargwadon ƙarfinsa. Sa'an nan ya tafi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

15 Ga guda, ya ba shi talenti biyar na kuɗi, ga wani talenti biyu, ga wani kuma talenti ɗaya, kowa bisa ga azancinsa. Sa’an nan ya yi tafiyarsa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 25:15
5 Iomraidhean Croise  

Da ya fara ƙididdigar, sai aka kawo masa wanda yake bi talanti dubu goma bashi.


“To, ga kuma wani misali. An yi wani maigida da ya yi garkar inabi, ya shinge ta, ya haƙa ramin matse inabi a ciki, ya kuma gina wata 'yar hasumiyar tsaro. Ya ba waɗansu manoma sufurin garkar, sa'an nan ya tafi wata ƙasa.


Wanda kuwa bai san nufin ubangijinsa ba, ya kuma yi abin da ya isa dūka, za a doke shi kaɗan. Duk wanda aka ba abu mai yawa, a gunsa za a tsammaci abu mai yawa. Wanda kuma aka danƙa wa abu mai yawa, abu mafi yawa za a nema a gare shi.”


Duk da haka dai, sai kowane ɗayanku ya ƙaunaci matarsa kamar kansa, ita matar kuwa ta yi wa mijinta ladabi.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan