Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 24:5 - Littafi Mai Tsarki

5 domin mutane da yawa za su zo da sunana, suna cewa, su ne Almasihu, har su ɓad da mutane da yawa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 Gama mutane da yawa za su zo cikin sunana, suna cewa, ‘Ni ne Kiristi,’ za su kuwa ruɗi mutane da yawa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 24:5
15 Iomraidhean Croise  

Ubangiji kuwa ya ce mini, “Annabawa, annabcin ƙarya suka yi da sunana. Ban aike su ba, ban kuwa umarce su ba, ban kuma yi magana da su ba. Annabcin da suke yi muku na wahayin ƙarya ne, dubar da suke yi marar amfani ce, tunaninsu ne kawai.


Ubangiji ya ce, “Ni ban aiki waɗannan annabawa ba, Duk da haka sun tafi, Ban kuwa yi musu magana ba, Amma sun yi annabci.


Na ji abin da annabawan nan suka ce, su da suke annabcin ƙarya da sunana. Suna cewa, ‘Na yi mafarki!’


Ni Ubangiji, na ce kada ku ruɗi kanku da cewa Kaldiyawa ba za su dawo ba, gama ba shakka za su zo.


Annabawan ƙarya da yawa za su firfito, su ɓad da mutane da yawa.


Don almasihan ƙarya da annabawan ƙarya za su firfito, su nuna manyan alamu da abubuwan al'ajabi, don su ɓad da ko da zaɓaɓɓu ma in dai zai yiwu.


Ni na zo ne da sunan Ubana, ga shi, ba ku karɓe ni ba. In da wani zai zo da sunan kansa, shi za ku karɓa.


Shi ya sa na ce muku za ku mutu da zunubanku. Domin in ba ku gaskata ni ne shi ba, za ku mutu da zunubanku.”


Sai Yesu ya ce, “Sa'ad da kuka ɗaga Ɗan Mutum, a sa'an nan ne za ku gane ni ne shi, ba na yin kome kuma ni kaɗai, sai dai Uba ya koya mini, haka nake faɗa.


Ya ku 'yan yarana, zamanin ƙarshe ne fa. Kamar yadda kuka ji, magabcin Almasihu yana zuwa, ko a yanzu ma, magabtan Almasihu da yawa sun zo. Ta haka muka sani zamanin ƙarshe ne.


Wane ne maƙaryacin nan, in ba wanda ya mūsa Yesu shi ne Almasihu ba? Irin wannan shi ne magabcin Almasihu, shi wanda yake ƙin Uban da Ɗan.


Duk ruhun kuwa da bai bayyana yarda ga Yesu ba, ba na Allah ba ne, wannan shi ne ruhun magabcin nan na Almasihu wanda kuka ji zai zo, a yanzu ma har yana duniya.


Duk mazaunan duniya kuma, za su yi mata sujada, wato, duk wanda, tun farkon duniya, ba a rubuta sunansa a Littafin Rai na Ɗan Ragon nan da yake Yankakke ba.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan