Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 24:43 - Littafi Mai Tsarki

43 Amma dai ku sani, da maigida zai san ko a wane lokaci ne da dare ɓarawo zai zo, da ya zauna a faɗake ya hana a shigar masa gida.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

43 Ku dai gane wannan, da maigida ya san ko a wane lokaci ne da dare, ɓarawo zai zo, da sai yă zauna a faɗake yă kuma hana a shiga masa gida.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 24:43
18 Iomraidhean Croise  

Da dare ɓarayi sukan kutsa kai cikin gidaje, Amma da rana sukan ɓuya, su guje wa haske.


Mijina ba ya gida, ya yi tafiya mai nisa.


Wajen ƙarfe uku na dare sai Yesu ya nufo su, yana tafe a kan ruwan tekun.


Da suka karɓa sai suka yi ta yi wa maigidan gunaguni,


To, ku zauna a faɗake fa, don ba ku san ranar da Ubangijinku zai dawo ba.


Don haka ku ma sai ku zauna a kan shiri, domin a lokacin da ba ku zata ba, Ɗan Mutum zai zo.”


Tun suna wajen sayen, sai angon ya iso, waɗanda suke shirye suka shiga wurin biki tare da shi, aka kuma rufe ƙofa.


Don haka, sai ku zauna a faɗake, don ba ku san ranar ba, ko kuwa sa'ar.”


To, ku zauna a faɗake fa, don ba ku san lokacin da maigidan zai dawo ba, ko da yamma ne, ko da tsakar dare ne, ko da carar zakara ne, ko da safe ne,


da ya ga suna fama da tuƙi, gama iska na gāba da su, misalin ƙarfe uku na dare sai ya nufo su, yana tafe a kan ruwan teku. Ya yi kamar zai wuce su,


In kuwa ya zo da tsakar dare ne, ko kuwa bayan tsakar dare, ya same su a faɗake, bayin nan masu albarka ne.


Amma dai ku sani, da maigida zai san lokacin da ɓarawo zai zo, da ya zauna a faɗake, ya hana a shiga masa gida.


Koyaushe ku zauna a faɗake, kuna addu'a ku sami ikon tsere wa dukan waɗannan al'amura da za su auku, ku kuma tsaya a gaban Ɗan Mutum.”


(“Ga ni nan a tafe kamar ɓarawo! Albarka tā tabbata ga wanda yake a zaune a faɗake, yana saye da tufafinsa, don kada ya tafi tsirara, a ga tsiraicinsa.”)


Don haka, sai ka tuna da abin da ka karɓa ka kuma ji, ka kiyaye shi, sa'an nan ka tuba. In ba za ka yi tsaro ba, zan zo kamar ɓarawo, ba kuwa za ka san a lokacin da zan auko maka ba.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan