Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 24:30 - Littafi Mai Tsarki

30 A sa'an nan ne alamar Ɗan Mutum za ta bayyana a sararin sama, duk kabilan duniya kuma za su yi kuka, za su ga Ɗan Mutum yana zuwa kan gajimare, da iko da ɗaukaka mai yawa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

30 “A sa’an nan ne alamar dawowar Ɗan Mutum zai bayyana a sararin sama, dukan al’umman duniya kuwa za su yi kuka. Za su ga Ɗan Mutum yana zuwa kan gizagizan sararin sama, da iko da kuma ɗaukaka mai girma.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 24:30
17 Iomraidhean Croise  

“A cikin wahayi na dare, na ga wani kamar Ɗan Mutum. Yana zuwa cikin gizagizai, Ya zo wurin wanda yake Tun Fil Azal, Aka kai shi gabansa.


“Zan cika zuriyar Dawuda da mutanen Urushalima da ruhun tausayi da na addu'a. Za su dubi wanda suka soke shi, har ya mutu. Za su yi makoki dominsa kamar waɗanda aka yi musu rasuwar ɗan farinsu.


A ran nan za a yi babban makoki a Urushalima kamar mutane suka yi wa Hadadrimmon a filin Magiddo.


Yana zaune a kan Dutsen Zaitun sai almajiransa suka zo wurinsa a kaɗaice, suka ce, “Gaya mana, yaushe za a yi waɗannan abubuwa? Mece ce kuma alamar dawowarka, da ta ƙarewar zamani?”


Kamar yadda aka yi a zamanin Nuhu, haka dawowar Ɗan Mutum za ta zama.


ba su farga ba har Ruwan Tsufana ya zo ya share su. Haka komowar Ɗan Mutum za ta zama.


Sai Yesu ya ce masa, “Yadda ka faɗa. Ina kuwa gaya muku a nan gaba za ku ga Ɗan Mutum zaune a dama da Mai Iko, yana kuma zuwa a kan gajimare.”


A sa'an nan ne za a ga Ɗan Mutum na zuwa cikin gajimare, da iko mai girma da ɗaukaka.


“Gaya mana yaushe za a yi waɗannan abubuwa? Wace alama kuma za a gani sa'ad da suke shirin aukuwa?”


A sa'an nan ne za su ga Ɗan Mutum yana zuwa a cikin gajimare da iko da ɗaukaka mai yawa.


Amma nan gaba, Ɗan Mutum zai zauna dama na Allah Mai iko.”


Sai suka ce, “Ya ku mutanen Galili, don me kuke tsaye kuna duban sama? Yesun nan da aka ɗauke daga gare ku aka kai shi Sama, zai komo ne ta yadda kuka ga tafiyarsa zuwa Sama.”


yă kuma ba ku hutu har da mu ma, ku da ake ƙuntata wa ɗin, a ranar bayyanar Ubangiji Yesu daga Sama tare da manyan mala'ikunsa, a cikin wuta mai ruruwa,


Ga shi, zai zo a cikin gajimare, kowa zai gan shi, har da waɗanda suka soke shi, duk kabilan duniya kuma za su yi kuka a kansa. Wannan haka yake. Amin.


Aka kuma ga wata babbar alama a sama, wata mace tana a lulluɓe da rana, tana a tsaye a kan wata, da kuma kambi mai taurari goma sha biyu a kanta.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan