“Ga shi, ina aiko da masunta da yawa,” in ji Ubangiji, “za su kuwa kama su, daga baya kuma zan aika da mafarauta da yawa, za su farauce su daga kowane tsauni, da tudu, da kogwannin duwatsu.
“Ni Ubangiji Allah na ce, kai ɗan mutum, sai ka gayyato kowane irin tsuntsu da dukan bisashe daga ko'ina, su zo idi wanda nake shirya musu a duwatsun Isra'ila. Za su ci nama su kuma sha jini.
“Dawakansu sun fi damisa sauri, Sun fi kyarketan maraice zafin hali, Sojojin dawakansu suna zuwa a guje. Sojojin dawakansu suna zuwa daga nesa, Sukan tashi kamar gaggafa da sauri don su cinye.
Ubangiji zai kawo wata al'umma daga nesa, wato daga bangon duniya, mai kai sura kamar gaggafa, wadda za ta yi gāba da ku. Al'ummar da ba ku san harshenta ba,