Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 24:24 - Littafi Mai Tsarki

24 Don almasihan ƙarya da annabawan ƙarya za su firfito, su nuna manyan alamu da abubuwan al'ajabi, don su ɓad da ko da zaɓaɓɓu ma in dai zai yiwu.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

24 Gama Kiristi masu yawa na ƙarya, da annabawan ƙarya za su firfito, su kuma aikata manyan alamu da ayyukan banmamaki don su ruɗi har da zaɓaɓɓu ma in zai yiwu.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 24:24
31 Iomraidhean Croise  

wato tsofaffi da manyan mutane su ne kawunan, ƙafafu kuwa su ne annabawan da suke koyar da ƙarairayi!


Gama da yawa ake kira, amma kaɗan ne zaɓaɓɓu.”


Annabawan ƙarya da yawa za su firfito, su ɓad da mutane da yawa.


Ba don an taƙaita kwanakin nan ba, da ba ɗan adam ɗin da zai tsira. Amma sabili da zaɓaɓɓun nan za a taƙaita kwanakin.


To, na dai gaya muku tun da wuri.


Zai kuwa aiko mala'ikunsa su busa ƙaho mai tsananin ƙara, su kuma tattaro zaɓaɓɓunsa daga gabas da yamma, kudu da arewa, wato, daga wannan bangon duniya zuwa wancan.”


domin mutane da yawa za su zo da sunana, suna cewa, su ne Almasihu, har su ɓad da mutane da yawa.


“Ku kula da annabawan ƙarya, waɗanda sukan zo muku da siffar tumaki, amma a zuci kyarketai ne masu ƙāwa.


Don almasihan ƙarya da annabawan ƙarya za su firfito, su nuna alamu da abubuwan al'ajabi, don su ɓad da ko da zaɓaɓɓu ma, in zai yiwu.


Ashe, Allah ba zai biya wa zaɓaɓɓunsa da suke yi masa kuka dare da rana hakkinsu ba? Zai yi jinkiri a wajen taimakonsu ne?


Yesu ya ce masa, “In ba mu'ujizai da abubuwan al'ajabi kuka gani ba, ba yadda za a yi ku ba da gaskiya.”


Duk wanda Uba ya ba ni zai zo gare ni, wanda kuwa ya zo gare ni ba zan kore shi ba ko kaɗan.


Nufin wanda ya aiko ni kuwa, shi ne kada in yar da kowa daga cikin dukkan waɗanda ya ba ni, sai dai in tashe su a ranar ƙarshe.


Dā ma kuwa Bulus ya ƙudura zai wuce Afisa cikin jirgin, don kada ya yi jinkiri a Asiya, domin yana sauri, in mai yiwuwa ne ma, ya kai Urushalima a ranar Fentikos.


In mai yiwuwa ne, a gare ku, ku yi zaman lafiya da kowa.


To, ina daɗin nan da kuka ji a game da ni? Don na shaide ku a kan lalle da mai yiwuwa ne da kun ƙwaƙule idanunku kun ba ni!


“Idan wani annabi, ko mai mafarki ya fito a cikinku, ya yi muku shelar wata alama ko mu'ujiza,


Duk da haka, ƙaƙƙarfan harsashin ginin nan na Allah ya tabbata, hatimin nan kuwa yana jikinsa cewa, “Ubangiji ya san nasa,” da kuma, “Duk wanda ya bayyana yarda ga sunan Ubangiji, to, yă yi nesa da aikata mugunta.”


wato, ku da ikon Allah yake kiyayewa ta wurin bangaskiyarku, domin samun ceton nan da aka shirya a bayyana a ƙarshen zamani.


Don haka, ya ku ƙaunatatuna, da yake kun riga kun san haka, ku kula kada bauɗewar kangararru ta tafi da ku, har ku fāɗi daga matsayinku.


Ya ku 'yan yarana, zamanin ƙarshe ne fa. Kamar yadda kuka ji, magabcin Almasihu yana zuwa, ko a yanzu ma, magabtan Almasihu da yawa sun zo. Ta haka muka sani zamanin ƙarshe ne.


Wane ne maƙaryacin nan, in ba wanda ya mūsa Yesu shi ne Almasihu ba? Irin wannan shi ne magabcin Almasihu, shi wanda yake ƙin Uban da Ɗan.


Mun sani kowane haifaffen Allah ba ya yin zunubi, kasancewarsa haifaffen Allah ita takan kare shi. Mugun nan kuwa ba ta taɓa shi.


Sai aka kama dabbar, da kuma annabin nan na ƙarya tare da ita, wanda ya yi al'ajabai a gabanta, waɗanda da su ne ya yaudari waɗanda suka yarda a yi musu alamar dabbar nan, da kuma waɗanda suka yi wa siffarta sujada. Waɗannan biyu kuwa aka jefa su da ransu a cikin tafkin wuta da ƙibiritu.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan