Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 24:22 - Littafi Mai Tsarki

22 Ba don an taƙaita kwanakin nan ba, da ba ɗan adam ɗin da zai tsira. Amma sabili da zaɓaɓɓun nan za a taƙaita kwanakin.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

22 “Da ba don an taƙaita kwanakin nan ba, da babu wani da zai tsira, amma saboda zaɓaɓɓun nan, za a taƙaita kwanakin.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 24:22
13 Iomraidhean Croise  

Ko da mutum ɗaya cikin goma zai ragu a ƙasar, shi ma za a hallaka shi. Zai zama kamar kututturen itacen oak wanda aka sare.” Wato kututturen alama ce ta tohuwar jama'ar Allah zuwa gaba.


Ni Ubangiji na ce sulusi biyu na ƙasar za su hallaka, Sulusi ɗaya ne kawai zai ragu.


Gama zan tattara dukan al'ummai su yi yaƙi da Urushalima. Za a ci birnin, a washe gidajen. Za a yi wa mata faɗe. Za a kai rabin mutanen birnin bauta, amma za a bar sauran mutanen a cikin birnin.


Gama da yawa ake kira, amma kaɗan ne zaɓaɓɓu.”


Don almasihan ƙarya da annabawan ƙarya za su firfito, su nuna manyan alamu da abubuwan al'ajabi, don su ɓad da ko da zaɓaɓɓu ma in dai zai yiwu.


Zai kuwa aiko mala'ikunsa su busa ƙaho mai tsananin ƙara, su kuma tattaro zaɓaɓɓunsa daga gabas da yamma, kudu da arewa, wato, daga wannan bangon duniya zuwa wancan.”


Da ba don Ubangiji ya taƙaita kwanakin nan ba, da ba ɗan adam ɗin da zai tsira. Amma sabili da zaɓaɓɓun nan da ya zaɓa, sai ya taƙaita kwanakin.


Ashe, Allah ba zai biya wa zaɓaɓɓunsa da suke yi masa kuka dare da rana hakkinsu ba? Zai yi jinkiri a wajen taimakonsu ne?


tun ba ta haifi 'ya'yan ba, balle su yi wani abu mai kyau ko marar kyau–don nufin Allah bisa ga zaɓensa ya tabbata, ba ga aikin lada ba, sai dai ga kiransa,


Don haka nake jure kome saboda zaɓaɓɓu, domin su ma su sami ceton nan da yake samuwa ta wurin Almasihu, a game da madawwamiyar ɗaukaka.


Daga Bitrus, manzon Yesu Almasihu, zuwa ga zaɓaɓɓun Allah da suke bare, a warwatse a Fantas, da Galatiya, da Kafadokiya, da Asiya, da kuma Bitiniya,


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan