Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 24:2 - Littafi Mai Tsarki

2 Amma ya amsa musu ya ce, “Kun ga duk waɗannan ko? Hakika, ina gaya muku, ba wani dutsen da za a bari nan a kan ɗan'uwansa ba a baje shi ba.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 Sai Yesu ya ce, “Kun ga duk waɗannan abubuwa? Gaskiya nake gaya muku, ba wani dutse a nan da za a bari a kan wani; duk za a rushe.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 24:2
8 Iomraidhean Croise  

“Mika kuwa, mutumin Moreshet, ya yi annabci a kwanakin Hezekiya, Sarkin Yahuza, ya faɗa wa dukan mutanen Yahuza cewa, “ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Runduna ya ce, Za a nome Sihiyona kamar gona, Urushalima kuwa za ta zama tsibin juji, Ƙwanƙolin dutsen Haikalin zai zama kurmi.’


Saboda ku kuwa za a nome Sihiyona kamar gona, Urushalima kuwa za ta zama tsibin kufai, Dutse inda Haikali yake zai zama kurmi.


su fyaɗa ku a ƙasa, ku mutanen birni duka, ba kuma za su bar wani dutse a kan ɗan'uwansa ba a birninku, don ba ku fahimci lokacin da ake sauko muku da alheri ba.”


Tun da yake duk abubuwan nan za a hallaka su haka, waɗanne irin mutane ya kamata ku zama? Ya kamata ku yi zaman tsarkaka masu ibada,


Ban kuwa ga wani Haikali a birnin ba, domin Haikalinsa Ubangiji Allah Maɗaukaki ne, da kuma Ɗan Ragon.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan